A yau Litinin ne Shugaba Muhammadu Buhari ya nada fitaccen masanin kwakwaf din sirrin tara harajin nan mai suna Muhammadu Nami shugabancin Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida, wato FIRS.
Nami ya gaji tsohon shugaban FIRS, Babatunde Fowler, wanda wa’adin aikin sa ya kare a yau Litinin. Ana sa ran Fowler zai damka iko a hannun daraktan da ya fi sauran ma’aikatan FIRS girman matsayi, wanda shi kuma zai rike, kafin Majalisar Dattawa ta amince da nadin Nami da Buhari ya yi.
Kakakin Yada Labarai na Shugaban Kasa, Garba Shehu, ya bayar da takaitaccen tarihin Muhammad Nami.
Kamar yadda Shehu ya bayyana, Nami kwararren masanin sirrin tara haraji ne, kuma kwararren akawu ne da ya yi ayyukan da suka cancanci jinjinawa da da cira masa tuta.
Ya shafe shekaru kusan 30 ya na aikin kididdigar bin diddigin alkaluman kashe kudade, shirya dabarun kirkiro hanyoyin samun kudaden haraji da kuma bada shawarwari ga bankuna, manyan masana’antu da ma’aikatatun gwamnati da kuma kungiyoyin bayar da agaji.
Kwararre ne matuka wajen bayar da shawarar da za a bi a kai gacin samun nasarar kafa sabbin masana’antu da masu zuba jarin harkokin kasuwanci.
Nami ya kammala Jami’ar Bayero da ke Kano cikin 1991, inda ya samu digirin farko a fannin Sanin Haayyar Dan Adam.
Cikin 2004 ya kammala digiri na biyu a fannin Ilmin Kasuwanci. Sannan kuma ya halarci Cibiyar Masana Tara Haraji ta Najeriya, sai Cibiyar Nazarin Yadda Ake Karbo Basussuka, kuma mamba ne Kungiyar Akantoci ta Kasa.
Nami ya fara aiki da PFK cikin 1993.
Har yanzu Muhammad na aiki da Hukumomi da Kwamitocin Hukumomin Binciken Kashe Kudade.
Cikin Nuwamba, 2017 Buhari ya nada shi mamba na Kwamitin Shugaban Kasa na Bankado Kudaden Sata da Kadarorin Sata.
Ya na da aure da iyali.
Discussion about this post