A dalilin rashin jituwa da ya kaure tsakanin wasu ‘yan sanda biyu a unguwan Dutse Alhaji da ke garin Abuja Sufeto din ‘yan sanda ya bindige wani na kasa dashi mai mukamin kofur.
Mataimakiyar kwamishinan ‘Yan sandan, Maryam Yusuf, ta bayyana cewa tuni har Kwamishinan ‘Yan sanda dame kula da wannan shiyya Bala Ciroma ya umarci shugaban wannan yanki ya gaggauta gudanar da bincike a kai.
Maryam ta ce a bisa rahoton binciken farko da aka yi, an gano cewa shi wannan Sufeto ya dirka wa Kofur din harshi ne da yayi sanadiyyar mutuwar sa sannan ya ji wa wani sufeto da ciwo.
Bayan haka ta yi kira ga mutanen wannan yanki da su kwantar da hankalin su, cewa rundunar zata yi cikakken bincike akai.