Hukumar tsaro na SSS ta saki mawallafin Jaridar Sahara Reporters dake tsare a hannun ta a bisa umarnin kotu.
Baya ga haka kuma hukumar ta biya shi Naira 100,000 kamar yadda kotu ta umurce ta.
Idan ba a manta ba Mai Shari’a Ijeoma Ojukwu ta Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta umarci jami’an SSS su saki Mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore cikin awoyi 24.
Yayin da ta ke yanke hukunci a yau Alhamis, Ijeoma ta ce haramun ne Sowore ya kara ko da kwana daya a hannun SSS.
Sannan ta ce shi ma wanda ake tuhumar su tare, mai suna Olawale Bakare a sake shi ba tare da bata lokaci ba.
Ba a nan ta tsaya ba. Mai Shari’a ta kuma umarci SSS su biya Sowore naira 100,000.
An ci su wannan tara ce sakamakon kin bin umarnin kotu da suka yi a ranar 6 Ga Nuwamba, inda kotu ta kara cewa su gaggauta sakin Sowore.
Ijeoma ta nuna bacin rai tare da gargadin SSS cewa bai yiwuwa don su na jami’an tsaro su rika take umarnin kotu, kuma su maida kan su tamkar wata kotu ta musamman.
Daga nan ta dage shari’ar zuwa ranar 6 Ga Disamba.
Tun cikin watan Agusta aka tsare Sowore, bisa zargin sa da kokarin shirya juyin turu a Najeriya, saboda shelar da ya yi na kiran a fito a yi #RevolutionNow.
Duk da sau biyu a baya kotu na bada umarnin a saki Sowore da Bakare, SSS sun ki sakin su.
Wannan ne karo na uku da kotu ta sake bada umarnin a sake su.
Ana tuhumar su da laifuka bakwai da suka hada har da yi wa Najeriya zagon-kasa, zamba, harkallar damfara ta intanet da kuma cin zarafin Shugaba Muhammadu Buhari.
Umarnin baya-baya da Ijeoma ta bayar dai, SSS sun kafa masa tsauraran sharudda, wadanda daba kuma aka ki sakin sa.
Sowore ya kasance a sahun gaban caccakar tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan a lokacin yakin neman zabe na 2015.
An rika yi masa da kuma jaridar sa kallon masu tsatstsauran goyon bayan Buhari.
Ya kasance cikin buya a lokacin mulkin Jonathan, inda ya fake a Amurka, bai dawo Najeriya ba sai bayan da aka sanar da cewa Buhari ne ya lashe zabe.