SSS na zargin Sowore na da alaka da Boko Haram, Shi’a da IPOB

0

Wata kwakkwarar majiya wadda ke da masaniyar garkamewar da aka yi wa mawallafin Sahara Reporters, Omoyele Sowore, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ana ci gaba da binciken sa ne akan zargin ya na da alaka da Boko Haram da sauran wasu kungiyoyin da gwamnatin tarayya ta haramta.

Wata majiya har guda biyu ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa zargin alaka da kungiyar ta’addanci na daga cikin ruwan tambayoyin da aka rika sheka wa Sowore a ofishin SSS a ranar 12 Ga Nuwamba.

“Jami’an tsaro sun matsa masa da tambayoyin neman ya shaida musu dangantaka ko alakar sa da Boko Haram, Kungiyar Kakudubar Neman kafa Kasar Biafra kuma ta Shi’a. Amma dai har yau ya na ci gaba da shaida musu cewa bas hi da wata akala da ko da daya daga cikin wadannan kungiyoyi.”

Yakin da gwamnatin Jonathan ce ta haramta Boko Haram da kuma gwamnatin Amurka tun cikin 2013, gwamnatin Buhari kuma ta haramta Shi’a da IPOB.

Sai dai kuma an yi ta cece-ku-cen haramta Shi’a da IPOB, kasancewa wannan kungiyar addini ce, wannan kuma kungiyar neman ‘yanci ce.

Labarin irin zargin da SSS ke wa Sowore ya fito kwanaki goma bayan da ‘yan Najeriya suka nemi a yi wa duniya bayanin dalilin sake kama Sowore da SSS suka yi, a ranar 6 Ga Disamba.

Wadannan tambayoyi da majiya ta ce an yi wa Sowore dai na nufin SSS sun fara shirya wani sabon fayil din bayanan sake gurfanar da Sowore bisa zargin aikata wasu laifukan daban, amma mai yiwuwa a gaban wata kotun, ba wadda ake ci gaba da shari’ar sa ba a yanzu.

An dai kama shi tun a ranar 3 Ga Agusta, bayan da ake zargin sa da kokarin shirya zanga-zangar #RevolutionNow, wadda gwamnatin tarayya ta ce yunkurin kifar da gwamnatin dimokradiyya ne.

Share.

game da Author