Wani abinda ke ci wa mutane tuwo a kwarya game da mulkin shugaba Muhammadu Buhari shine yadda gwamnatin ke neman rikidewa zuwa gwamnatin kama karya ganin yadda take wancakali da umarnin kotu da karya doka gaba-gadi ba tare da ta nuna halin ko in kula ba.
Kiri-Kiri jami’an hukumar tsaro na sirri, SSS, suka far wa kotun kasa a ranar 6 ga watan Disamba. Wannan abu da suka yi karya dokar kasa ce jami’an tsaro su afka kotu har cikin kotu domin cafke shi.
A dalilin kokarin su cafke mawallafin jaridar Sahara Reporters da kotu ta bada belin sa, jami’an SSS sun afka cikin kotun dauke da bindigogi inda suka nemi su tafi da shi da karfin tsiya duk da hakan ya haramta musu bisa ga dokar kasa.
A dalilin afkawa cikin kotu da jami’an tsaro suka yi ci wa dokar kasa fuska ne da kuma gurgunta tsarin mulkin dimokradiyya, duk a kokarin ganin sun kama Sowore, ya yi matukar barin baya da kura, domin ana ta yin suka da yin tir ga wannan mummunar abu da jami’an tsaro suka aikata.
Tun bayan wannan tabargaza da SSS suka aikata aka rika cewa tun da aka kafa kasa Najeriya, har zuwa lokuttan mulkin soja da aka yi da dama ba a taba samun wani lokaci da aka yi gwamnatin da jami’an tsaro suka yi wa dokar kasa katsalandar kuma suka karya ta son rai kamar irin abinda suka yi a kotun Najeriya ranar 6 ga watan Disamba.
Jim kadan baya haka sai gashi kakakin hukumar SSS Peter Afunanya ya fito karara ya musanta cewa wai duk abinda aka yi karya ne, yana mai cewa wai Sowore ne ya shirya haka domin a ga laifin jami’an SSS amma basu afka cikin kotu ba.
Abin kunya ne da rainin wayau a ce wai hukumar SSS za ta fito ta rika bayyana cewa wai wannan tabargaza da jami’anta suka yi shirya wa Sowore yayi bayan anyi wannan abu ne a gaban kungiyoyin Rajin Kare Hakkin Dan Adam, ‘Yan jarida, Lauyoyi, da mutane da dama kiri-kiri.
Bai kamata ace wai a irin wannan ci gaba da aka samu ba a duniya kuma hukuma kamar SSS ta rika fitowa tana karyata abinda jami’anta suka yi a kotu bayan bidiyoyin da aka rika dauka a lokacin da suka aikata wannan abin kunya ya karade ko-ina sannan su rika cewa wai ai bai auku. Karya ake mata.
Mai shari’a Ijeoma Ojukwu, ta yanke hukuncin bada belin Sowore kuma ta umarci hukumar SSS ta biya shi naira 100,000 a dalilin tsare shi da tayi na babu gaira babu dalili.
Muna cikin tashin hankali da damuwa matuka ganin cewa hukumar SSS karkashin shugabancin Yusuf Bichi ta rika karya dokar kasa a lokutta da yawa, Ciki har da cin zarafin mutane da tauye musu hakki da damar da dokar kasa ta basu. Tun da Bichi ya dare kujerar shugabancin hukumar SSS, hukumar ta fara yi wa dokar kasa hawan kawara, ta na keta umarnin kotu yadda ta ga dama.
Wadannan abubuwa sun tabbatar karara cewa zaman Bichi a wannan hukuma zai ci gaba da dagula matsayin dimokradiyya d girmama dokar kasa ne a kasar nan.
Lokaci yayi da Bichi zai duba mutunci da darajar kasar nan da mutanenta ya sauka daga kujerar shugabancin hukumar SSS saboda gazawarsa. Sannan kuma muna kira ga hukumar ta nemi gafarar ‘yan Najeriya da kuma fannin shari’ar kasar nan.
Sannan kuma muna kira ga hukumar da ta fito ta roki yan Najeriya da kuma fannin shari’a ta kasa.
Sannan kuma fadar shugaban kasa ta saka mutane cikin rudani matuka, ba mutanen Najeriya ba kawai duk duniya ne ake mamakin wannan abu da SSS suka yi.
Da farko dai kakakin fadar shugaban Kasa Garba Shehu ya yi ikirarin cewa fadar shugaban kasa bata ba da umarnin a sake cafke Sowore ba bayan beli da kotu ta bashi.
Sannan daga baya kuma suka sake fitowa suka ce hauragiyar Sowore tsakanin sa ne da Hukumar SSS saboda haka bai kamata mutane su rika mamakin abinda SSS suka yi masa ba.
Wannan shine kalaman da fadar shugaban kasa suka fiddawa suna cukuikuye kansa.