A kokarin far wa garin Biu a karo na biyu da Boko Haram suka yi kokarin yi, Sojojin Najeriya sun budewa Boko Haram din wuta babu kakkautawa.
Da misalin karfe 6 na yammacin Talata ne Boko Haram suka far wa wasu kauyuka biyu dake kusa da garin Biu inda suka kashe mutane biyu sannan wasu 13 suka tsira da rauni a jikin su.
Dama a cikin wannan mako Boko Haram sun yi kokarin shiga garin Biu amma hakan ya gagara saboda artabu da suka yi da dakarun Najeriya, inda suka fatattake su.
Wani dan banga dake aikin sa kai a garin Biu ya shaida wa manema labarai cewa Boko Haram sun yi dafifi a kusa da garin Biu suna shirin far wa garin.
” Sai dai burin su bai cika ba domin dakarun Najeriya sun far musu. Yanzu haka rukugin harsashi kawai kaje ji ana bari.
Mataimakin gwamnan jihar Barno Umar Kadafur, wanda dan asalin garin Biu ne ya isa garin domin bukin Kirsimeti. Bayan haka ya ziyarci asibitin da wadanda Boko Haram suka ji wa rauni a harin da suka kai.