Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Ogun sun damke saurayin wata dalibar Jami’ar Jihar Lagos tare da mahaifiyar sa da wani boka.
An damke su ukun ne bisa tuhumar su da laifin kashe dalibar, wadda ke shekarar karshe tare da yin tsafi da wasu sassan jikin ta.
An dai kama saurayin mai su na Adeeko Owolabi da bokan da ya yi masa tsafi da gawar dalibar mai suna Favour Daley-Oladele bayan sun kashe ta.
Saurayi Ya Kwankwstse Kan Budurwa Ta Na Barci
Wannan lamari ya yi muni matuka, domin ganin ‘yar su Favour ba ta dawo gida ba tsawon lokaci, sai suka kai rahoto ofishin DPO na ‘yan sandan Mowe, su kuma suka shiga bin diddigin binciken yadda aka yi ta bace har aka daina jin duriyar ta.
Da farko dai kamar yadda Jami’in Yada Lanarai na ‘Yan Sandan Ogun, Abimbola Oyeyemi ta tabbatar a yau Lahadi, ta ce ”yan sanda sun fara da binciken wurin da ta je a karshen ganin ta da aka yi.
Sun gano cewa ta je gidan wani Fasto ne mai suna Segun Philip a garin Moro cikin Jihar Osun. Cocin dai kamar yadda jami’an tsaron suka shaida, irin na masu bautar nan ne sanye da fararen jallabiya, da ake kira ‘White
garment Church.’
Isar ‘yan sanda cocin ke da wuya sai suka cumuimuyi fasto, inda bayan ya sha tambayoyi, sai ya ce tabbas Favour ta zo gidan sa, amma saurayin ta ne ya kawo masa ita.
Duk abin nan shi ma saurayin ashe ya na cocin, inda shi ma aka damke shi.
Favour Na Barci Na Kwankwatse Kanta -Saurayin ta
Saurayin Favour ya shaida cewa a ranar da ya kai wa fasto din budurwar ta sa, ta na cikin barci sai fasto ya ba shi kulki ya rika dankara ma ta a kai, har ta mutu.
Bayan ta mutu ne sai fasto ya dauko wuka da gatari ya datse ma ta kai. Sannan kuma ya farke cikin ta, ya ciro hantar ta, ya yi tsafi da ita, sannan ya ce saurayin ya je shi da mahaifiyar sa su cinye.
Saurayin Favour ya shaida wa ‘yan sanda cewa fasto ya ce idan suka ci hantar, to duhun talaucin da ya baibaye su zai yaye, hasken makudan kudade zai baibaye su.
Ya ce talauci ya afka wa mahaifiyar sa shekaru da dama, tun bayan rasuwar mahaifin su.
Yanzu dai Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Ogun, Kenneth Ebim ya bada umarnin a maida wannan batu a babbar hedikwatar ‘yan sanda ta jihar, bangaren binciken masu aikata manyan laifuka.