Sarki Sanusi ya amince da nadin da gwamna Ganduje ya yi masa

0

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya amince da nadin da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya yi masa shugaban majalisar sarakunan Kano.

Idan ba a manta ba gwamna Ganduje ya umarci Sarki Sanusi ya amsa takardar da aka aika masa na shugabantar kwamitin majalisar sarakunan jihar da bai yi ba.

Takardar wadda babban sakataren ma’aikatar ayyukan musamman na jihar ya saka wa hannu ta umarci sarki Sanusi ya amsa wannan takarda nan da kwana biyu ko ya gamu da fushin gwamnati.

Wani hadimin sarki Sanusi da baya so a fadi sunan sa domin ba a bashi damar cewa komai a kai ba ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa sarki Sanusi ya rungumi kaddara, ya bi umarnin gwamna Ganduje.

Sai dai kuma ya karyata takardar da ake ra yadawa wai ta fito daga fadar sarkin Kano ne.

Hadimin ya ce babu wata takarda da ya fito daga fadar sarki.

Kakakin gwamnatin jihar Salihu Yakasai ya tabbatar da wasikar sarki Sanusi.

Sai dai har yanzu ba a san kobyaushe sarki Sanusi zai kira taron majalisar sarakunan jihar ba.

Share.

game da Author