Jiya ne dubban matasa a garin Akure, babban birnin jihar Ondo suka banka wa wani katafaren coci wuta, tare da lalata ilahirin kayan da ke cikin cocin, ciki gar da daruruwan kujeru na zama.
Sun huce haushin su ne a kan cocin Sotitobire Miracle Centre na Akure, bayan zargin sace wani jinjiri mai shekara daya, mai suna Gold Kolawole tun a ranar 10 Ga Nuwamba, 2019.
A yanzu haka dai shugaban cocin, Alfa Babatunde na can kulle a hannun SSS dangane ya yadda aka yi yaro ya bace a cikin cocin sa.
Baya ga kone cocin Babatunde da aka yi, an kuma kone gidan sa duk a jiya Laraba, tare da baza ji-ta-ji-tar cewa an tono gawar yaron a cikin cocin.
Jami’an ‘yan sanda dai sun ce karya ce, ba a gano gawar yaro a cikin cocin ba. Sai dai kuma mafusata sun kashe dan sanda daya, an kona ofishin ‘yan sanda da kuma kashe wani mutum daya.
Iyayen yaron ne da kann su suka shigar da korafi a wajen SSS saboda zargin ‘yan sanda sun ki tabuka abin kirki, don ganin sun gano inda yaron su ya ke.
An kama fasto mai cocin kuma ana ci gaba da tsare shi, duk kuwa da ya ce ba shi hannu a batan yaron, sannan kuma an kamo wasu mambobin cocin duk su na tsare a hannun SSS.
Mahaifiyar jinjirin mai suna Modupe Kolawole, ta shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho cewa an dauke yaron ta ne a coci a lokacin da suke tsakiyar bauta.
“Amma duk da mu na ci gaba da nema haikan, har yau ba mu fidda rai ba cewa za mu gano da na.”
Yadda Abin Ya Faru
Modupe ta shaida wa PREMIUM Times cewa ranar Lahadin da abin ya faru, ta je coci da jinjirin na ta, amma sai ta bi shawarar masu kula da cocin, suka ce mata ta kai yaron ta can inda ake ajiye kananan yara.
“Bayan an tashi daga coci, kowa ya je ya na daukar yaron sa, ya na tafiya gida. Amma da na je inda suka ce na ajiye shi, na neme shi ko sama ko kasa, ban gani ba.”
Nan take Modupe ta kwartsa ihu ta na karaji, kuma ta garzaya wajen shugabannin cocin. Amma har yau babu ko labari.
Modupe ta fara zuwa cocin ne a farkon watan Yuni, bayan da wata kawar ta ta ba ta shawarar cewa idan ta na zuwa cocin, to tabbas za ta ga budin rayuwa ita da mijin ta.
A kokarin sun a gano dan su, har gaban babban basaraken Akure, wato Deji na Akure suka kai kara. Deji ya sa aka yi tsinuwa a kan duk wanda ke da hannu a satar yaron, to bala’i ya afka a kan sa.
Mai cocin dai Alfa Babatunde ya yi rantsuwa a fadar cewa ba shi da hannu a bacewar yaron.
Zargi
Ta ce an sha cewa ta rika kai dan ta wajen da ake zaunar da kananan yara, amma ta na kin kais hi, saboda dan na ta bai fara tafiya ba.
Amma a wannan ranar sai ta canja tunani, ta ce bari ta rika kai shi can a cikin yara, watakila ma zai koyi tafiya, idan ya ga wasu kananan yaran su na tafiya da kafafun su.
A wannan rana ta je ta ajiye yaron na ta a bangaren kuma ta yi rajistar cewa ta ajiye yaron ta mai suna Gold a bangaren na kula da kananan yara a cocin.
Ta ce lokacin da rana ta yi kafin a tashi, ta je wurin kula da yaran, amma sai ta ga an sauya musu yanayin wuraren zama, kuma an ba shi abincin da ita ta na ganin bai kamata a bai wa dan ta ba. Ta shaida wa masu kula da yaran ba ta amince da abincin ba, domin a cikin kwanon abincin sa akwai wadataccen abin da ta je masa da shi.
“Amma lokacin da aka tashi, da na je sai ban ga yaro na ba, kuma dukkan mutane 14 masu kula da yaron, kowa ya ce bai san yadda aka yi da dan nawa ba.”
Bayan ta gaji da guje-gujen bin motoci masu fita cocin ta na dubawa ko akwai dan ta a ciki, a haka dai Modupe ta hakura.
Ta yi zargin an shirya sace yaron na ta ne a cocin, domin da ta je duba shi kafin a tashi, ta samu an canja masa wuri daga inda ta ajiye shi.
Sannan kuma an ba shi wani abinci ya na ci, wanda ita dai ta ce bai kamata dan na ta ya ci ba, sannan kuma masu kula da yaran sun san ta ajiye masa na sa abincin da ya kamata su ba shi, amma ba su ba shi ba. Sai suka ba shi wani daban.
“Na zargi wani da na yi tunanin wani karan-kada-miya ne a cocin, sai daga baya na gano ashe wani babban jigo ne a cocin. Lokacinn da mu ka je, ya yi ta daukar hoton dan na wa, kuma ya yi ta kokarin ya san wasu bayanai dangane da mahaifin yaron.
Rufa-ido A Coci
“Inda na kara zargin da hadin bakin masu cocin aka sace yaro na, watau daidai lokacin da zan iya cewa sannan ne aka sace shi, ana cikin idaba sai fasto ya ce zai yi addu’ar minti 30, kuma kowa ya rufe idon sa. Wanda bai rufe ba inji faston wai zai mutu.
“A wannan lokacin kuma na fahimci wannan da ya rika daukar hoton dan nawa, kuma a cocin ya ke zaune a baya na, to da aka ce kowa ya rufe idon sa, sai na fahimci ba ya bayan nawa.
“To an agama addu’a bayan na bude ido na, sai na garzaya wajen yara, amma ina zuwa na nemi yaro na sama ko kasa, ban gan shi ba.
“yayin da ake neman yaron har cikin dare, sai kuma na fahimci a wannan lokacin babu wanda ya rika sagarabtun shiga ofsihin faston sai shi wannan mutumin da ya rika daukar hoton yaron nawa. Kuma duk karakainar shigar da ya ke yi a cikinn ofishin fasto, ya na tafe ya na daddanna wayar sa.
Walle-walle
“Wani abin daure kai kuma shi ne a lokacin da mu na ofishin ‘yan sanda da kuma ofishin SSS, wannan mutumin ya zo a cikin motar fasto.
Sannan kawai daga baya sai fasto ya kawo wani mutum daban da wai shi ake zargi, ba shi wannan da yari kara daukar hoton sa. Shi sai muka daina ganin sa. Kuma na san shi, dangi na ma sun gane shi, irin yadda ya rika haba-haba da dan nawa.
Mun yi kokarin jin ta bakin Kakakin Yada Labarai na SSS na Kasa a Abuja, amma har yanzu dai bai maido amsar tambayoyin da aka tura masa ta sakonn tes ba.
Discussion about this post