Da sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Dukkan godiya sun tabbata ga Allah. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Annabi Muhammad (SAW), da Iyalan sa da Sahabban sa baki daya.
Assalamu Alaikum
Ya ku ‘yan uwa masu girma da daraja, kun san ance idan kana raye a cikin duniyar nan to lallai zaka ji ko ka ga abubuwa na ban mamaki.
Duk da irin namijin kokarin da wasu bayin Allah suke yi na ganin cewa an kawo karshen rikicin da ke faruwa tsakanin Masarautar Kano da Gwamnatin Jihar Kano, wasu bata-gari suna nan suna ta kulle-kullen sharri da makirci, ta hanyar yada karya da kazafi, domin ganin lallai wannan yunkuri ya wargaje. Kasancewar, su a wannan rikicin ne suke cin abinci, a cikin sa ne suke sha, a cikin sa ne suke yin sutura har su dauki dauyin karatun ‘ya ‘yan su. Shi yasa suka sha alwashin ganin sai sun yiwa wannan shiri kafar ungulu!

Ya ku jama’ah, yau kuma mun wayi gari da wani sharri da kazafi da wasu shedanu da ake zargin sun fito ne daga cikin Gwamnatin Jihar Kano, suke yada wa. Sun yi wani rubutun karya domin bata sunan Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II. Wai suke cewa, Mai Martaba Sarki ya ziyarci Babban mai Shari’a na kasa, ya durkusa, yana rokon sa da a soke zaben Gwamna Ganduje a kotun koli! Jama’ah, wallahi ai kun san, idan mai fadar wannan magana ya zama wawa, soko, to ai ku masu saurare da karatu ba wawaye ba ne, ko sokwaye. Yaushe ne Mai Martaba Sarki zai yi wannan? Amma ai alhamdulillahi, shi babban mai Shari’ar yana nan raye bai mutu ba. Sai ya fadi lokacin da Mai Martaba Sarki ya kai masa wannan ziyarar, har ya roke shi da a soke zaben Gwamna.
Don Allah, don Allah, don Allah, wai me yasa mutane basu tsoron Allah ne? Kawai za su yi ta rubuce-rubucen karya da kazafi da sharri, don su bata sunan Mai Martaba Sarki, don su zubar masa da mutunci a biya su ‘yan kudin da ba zai yi masu maganin talaucin da ke damun su ba?
Yaku ‘yan uwa, ga abunda wadannan miyagun suka rubuta. Na kawo shi yadda suka rubuta shi a kammale, ba tare da na canza komai daga cikin rubutun nasu ba, suka ce:
“Da Dumi Dumin sa!!! Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II Ya Roki Babban Mai Shari’a Na Kasa Da A Soke Zaben Ganduje A Kotun Koli. Wani abin mamaki da ban takaici da ban haushi, gami da raina hankalin mutane, Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, a daidai lokacin da yake biyowa ta karkashin kasa yana rokon mutane masu daraja da kima daga wajen jihar Kano, da suzo a ba Gwamna Abdullahi Umar Ganduje hakuri, sai kuma ga shi Sarkin na Kano yaje wajen Babban Mai Shari’a na Kasa yana rokon sa Allah Annabi da a soke zaben Gwamna Ganduje a Kotun Koli, Idan lokacin yanke Shari’ar da jam’iyyar PDP da dan takarar Gwamna na jam’iyyar tsagin Kwankwasiyya, Abba Kabir Yusuf su ka kai, yayi. Hakan a cewar majiyar mu, ya girgiza wadancan bayin Allah da Sarkin yaje ya gayyato daga wajen Kano, saboda ya ga tusa ta kurewa bodari. Kuma wuta ta taho masa ganga-ganga za ta lakume shi. Har ta kai wasu daga cikin wadancan dattawa masu daraja daga wajen Kano, sun fara tantamar Sarkin na Kano, cewar kar yazo ya basu kunya. Amma dai har yanzu ba su fito sun fitar da wata matsaya ba kan hakan. Ance da Sarkin ya samu babban mai Shari’ar, shi babban mai Shari’ar an ruwaito cewar bai ba Sarkin fuska ba. Hasali ma nunawa Sarkin yayi cewar shi baya katsalandan kan harkokin Shari’a. Majiyar tamu ta kara da cewar haka Sarkin ya tashi ba laka gaba daya a jikin sa. Mutane suna ta cewa wannan abin kunya da kiyayya har ina kuma. Yanzu babban abinda ya rage shine, a ga dawowar mai girma Gwamnan Kanon, Ganduje, domin a ga yadda ma wancan kwamitin su Janar Abdussalamu Abubakar za su fuskance shi. Koda yake ana zargin cewa wasu daga cikin ‘yan kwamitin ma sun janye hannun su daga harkar gaba daya. Ido ne namu mu dai kam!!!!
Jama’ah wannan shine soki-burutsun da suka rubuta. Kuma wallahi kowa yasan wannan karya ce tsagwaron ta!
Kawai wannan tsokana ce daga bangaren wadanda basu son a shirya wannan matsala ko a gyara ta. Amma kuma Allah yafi su. Duk wanda yake tare da Allah, mutum ba zai iya yi masa komai ba.
Sannan sun yi rubutun nasu ne da harshen hausa, domin sun san cewa idan sun yi da turanci, to shi kansa Babban mai Shari’ar da sauran manyan kasa zasu gani. Kawai manufar su ta yada wannan kazafi, ita ce zubar da mutunci da kimar Mai Martaba Sarki, tare da bata masa suna!
Da wadannan mutane sun san hadari da bala’in da ke tattare da yiwa Musulmi sharri da kazafi, da wallahi ba su yi wannan rubutun ba. Ina rokon Allah ya shirye su, amin.
Ga bayanin Shari’ar Allah game da hadarin kazafi:
Daga cikin zunubai guda bakwai masu girma, masu halakar da wanda yake ta’ammuli dasu, wadanda Annabi (SAW) ya lissafa akwai yiwa Musulmi sharri da kazafi.
Kazafi shine: Kirkirar abun da mutum bai yi ba ko bai fada ba a jingina masa ace shine ya fada, ko jifan mutum da aikata alfasha ta zina, ko kore juna biyu ko kore Da ba tare da an bayar da cikakkun shaidu ba.
A lokacin da mutum ya jefa kansa a cikin irin wannan halayya ta yiwa mutane kazafi, to lallai ya sani, ya jefa kansa cikin halayyar da take halakar wa, domin yin kazafi ba karamin bala’i bane.
Da ace kotunan mu na Shari’ar Musulunci suna aiki yadda ya kamata, kuma ya kasance yadda za’a hukunta talaka haka za’a hukunta babba, kuma komai matsayin sa a cikin al’ummah, to a lokacin da mutum yayi wa wani kazafi lallai ya tsokano tsuliyar dodo, domin dole ne sai ya kawo cikakkun shaidu na mutane hudu maza Musulmai da zasu bada shaida akan hakan, idan kuma bai kawo shaidu ba, ko kuma ya kawo amma basu cika ba, to bulala tamanin (80) za’a yi masa.
Wannan tsari da Musulunci yake dashi ba karamin tsari bane, an samar da shi ne domin kare mutuncin mutane. Masu iya magana suna cewa mutunci madara ne in ya zube bai kwasuwa. Addinin mu na Musulunci mai albarka, yana daga cikin manyan manufofin sa kare mutunci, wannan yasa Musulunci ya dauki irin wannan mataki.
Idan ka tsaya ka kalli ayoyin da suka yi magana akan hadarin kazafi, zaka gan su kashi uku ne, kuma duk suna cikin Suratun Nur.
Kashi na farko: Aya ta: 4-5, Allah Madaukakin Sarki yana cewa:
”Wadanda suke jifan mata masu kamun kai (da zina) sannan kuma basu kawo shaidu hudu ba to kuyi masu bulala tamanin (80), kuma kada ku sake karbar shaidar su har abada, kuma wadannan sune fasikai. Sai dai kawai wadanda suka tuba bayan haka kuma suka kyautata, to lalle Allah mai yawan gafara ne kuma mai yawan jin kai.”
A nan Allah madaukakin Sarki ya bayyana hukuncin duk mutumin da ya yiwa mace ko namiji kazafi kuma bai iya kawo shaidu hudu ba, sai Allah ya bayyana hukuncin da za’a yi masa. Abu na farko bulala tamanin (80), abu na biyu ba za’a sake karbar shaidar sa ba har abada, abu na uku kuma wannan mutumin fasiki ne, sai idan ya tuba. To anan ne Malamai suke maganar shin idan ya tuba za’a ci gaba da karbar shaidar sa, kuma shike nan shi ba fasiki bane? Amma dai mu sani, ko ya tuba sai an yi masa bulala tamanin.
Kashi na biyu: Ayoyin da suka yi bayanin mijin da ya yiwa matarsa kazafi kuma bai iya kawo shaidu ba to shi tsinuwa za su yi, shi da matar tasa. Allah Ta’ala yana cewa:
”Wadanda kuma suke jifan matan su (da zina) kuma ya kasance basu da shaidu sai dai su karan kan su, to shaidar dayan su (ita ce) rantsuwa hudu da Allah, lalle shi yana cikin masu gaskiya, (a rantsuwa) ta biyar sai yace tsinuwar Allah ta hau kansa idan ya kasance cikin makaryata. Kuma abinda zai hana ayi mata azaba (haddi) shine (ita ma) ta yi rantsuwa hudu da Allah cewar lallai shi (mijin) yana cikin makaryata, (a rantsuwa) ta biyar, ta ce lallai fushin Allah ya tabbata a kanta idan (mijin na ta) ya kasance cikin masu gaskiya.” [Suratun Nur, aya ta: 6-8]
A nan Allah Madaukakin Sarki yayi bayanin idan miji ya yiwa matarsa kazafi kuma bai iya kawo shaidu hudu ba to ‘Li’ani” za su yi. Amma duk wanda ba miji bane to kodai ya kawo shaidu mutane hudu maza Musulmai ko kuma ayi masa bulala tamanin, babu maganar shi wanda aka yiwa kazafi ya rantse idan ba haka bane, ko kuma shi da yayi kazafin cewa ya rantse duk babu ko dai shaidu ko bulala tamanin.
Kashi na uku: Ayoyin da suka yi magana akan kazafin da aka yiwa mata muminai, masu kamun kai, natsattsu, kammalallu, to wadannan masu yiwa irin wadannan matan kazafi tsine masu aka yi duniya da lahira. Allah Madaukakin Sarki yana cewa:
”Lallai dukkanin wadanda ke jifan mata masu kamun kai gafalallu (daga aikata alfasha) wadanda suke muminai, to an tsine masu a duniya da kuma lahira, kuma suna da azaba mai girma. A ranar da harsunan su za su bada shaida a kan su da hannayen su, da kuma kafafuwan su, ta sanadiyyar abinda suka kasance suna aikatawa. A wannan ranar ce Allah zai cika masu sakamakon su na gaskiya, kuma za su sani lallai Allah shine wanda yake mai gaskiya kuma mai bayyanar da abubuwa.” [Suratun Nur, aya ta: 23-25]
Wannan ya nuna mana shi karan kansa kazafin ya kasu kashi-kashi, kashi na farko, shine yiwa gama-garin mutane wadanda suke suna da kyawawan halaye da kuma wanda ba’a rasa ba, su aka anbaci hukuncin yi masu kazafi a kashin farko, sai kuma wanda ya kasance tsakanin miji da mata. Sai wannan kashi na uku, wanda mutum zai ga mace ko namiji mai kamun kai, mai addini, natsattse, mumini, kawai ya antayo ashar ya watsa mata/masa, ya dinga fadan wasu maganganu na karya, wadanda da za’a tara masa dukkan arzikin duniyar nan domin ya kawo shaida akan haka wallahi ba zai iya ba. Domin wani ya dauka irin halin da yake da shi to kowa haka yake, to kaga bayan ya kasa kawo wadannan shaidu za’a yi masa hukuncin kazafi anan duniya, sannan kuma ya jira ranar alkiyama, domin Allah baya bari a taba bayin sa na kwarai.
Ya Allah, ka sa mu daga cikin su, ka kare mu daga sharrin masharranta, ka tsare mu, ka tsare muna imanin mu da mutuncin mu, ka kare imani, da martaba da mutuncin Mai Martaba Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II, amin.
Daga wadanna takaitattun bayanai da suka gabata, ya bayyana a gare mu, fili, karara, irin yadda addinin Musulunci ya dauki mutunci da daraja da kima, ya karewa kowa mutuncin sa, domin idan ba haka ba, sai kowa ya fadi duk abinda ya ga dama, ko kuma wasu su sa shi ya fada, yana ganin cewa ai bai wuce aci tarar sa ba, amma idan yasan cewa zai sha bulala ne, to dole ya shiga taitayin sa, yasan me zai fada, sai ya zama ya kare mutuncin sa da na zuri’ar sa, kamar yadda ya kare mutuncin wani da na zuri’ar sa.
Wassalamu Alaikum,
Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuta daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.