An nada kwamitin dattawan Arewa domin shiga tsakanin rikicin masarautar Kano da yaki ci yaki cinyewa.
Tsohon shugaban kasa Abdussalami Abubakar ne zai shugabanci wannan kwamiti. Sannan kuma an saka gwamnonin Ekiti, Kayode Fayemi da Aminu Masari a matsayin mambobi.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da:
Alh. Adamu Fika, Wazirin Fika, CFR
Gen. Muhammadu Inuwa Wushishi, CFR, GCON
Alh Abdullahi Ibrahim, SAN
Dr. Dalhatu Sarki Tafida, OFR, CFR
Dr. Umaru Mutallab, CON
Prof. Ibrahim Gambari, CFR
Sheikh Sharif Ibrahim Saleh
Dr. Adamu Fika – Secretary
Idan ba a manta ba tun bayan derewar gwamna Ganduje kujerar gwamnan jihar Kano a karo ta biyu, ya fara takun saka da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi.
Babban dalili kuwa shine wai Sarkin Kano Sanusi bai mara masa baya ba a zaben 2019.
Gwamna Ganduje ya fara da ne da kirkiro sabbin masarautu domin rage wa sarki Sanusi karfin mulki a Kano.
Kwamitin sun yi kira ga magoya bayan sarki Sanusi da gwamna Ganduje da su daina sukan juna ko kuma rubuce-rubucen batanci ga juna. Su yi hakuri a kai ga samun matsaya ga wannan matsala.
Discussion about this post