Rikicin Makiyaya da Manoma: An kashe mutum daya wasu sun ji rauni jihar Jigawa

0

A dalilin rikicin da ya barke tsakanin wasu makiyaya da manoma a karamar hukumar Birnin Kudu a jihar Jigawa mutum daya ya mutu wasu da dama sun jikkata.

Shugaban kungiyar makiyaya ‘Miyetti Allah’ reshen jihar Sa’idu Gagarawa ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan wani dan achaba ya buge dan wani makiyayi.

Gagarawa ya ce a dalilin haka kuwa makiyayan karamar hukumar suka kashe wannan dan achaban.

Bayan haka jami’in yada labarai na karamar hukumar Sanusi Doro ya bayyana wa manema labarai cewa bayan kashe wannan dan achaba da Fulanin suka yi sai rikici ya barke tsakanin manoma da makiyaya.

Doro ya ce Fulanin dake karamar hukumar duk sun arce gudun kada manoman su kawo musu harin daukan fansar dan uwan su da ya rasu ba shiri.

Kakakin ‘yan sanda Audu Jinjiri ya tabbatar da haka sannan ya fadi sunan dan achaban da aka kashe a matsayin Abubakar Dauda mai shekaru 38.

“Mun samu labarin cewa rikici ya barke tsakanin wasu makiyaya Fulani da manoma a Bodala rugan Fulani inda aka sari wani bahaushe Abubakar Dauda da adda.

“’yan sanda sun kai Dauda babbar asibitin Hadeja inda a nan ne Dauda ya ce ga garin ku nan.

Ya ce an zuba jami’an tsaro a karamar hukumar sannan zaman lafiya ya fara dawowa wannan kauye.

Jinjiri yace rundunar ta fara gudanar da bincike sannan har ta yi nasaran kama wani Usman Isah mai shekaru 30 dake zama a Bodala.

Share.

game da Author