NYSC ta tura dalibai 879 bautar kasa a jihar Barno

0

Akalla dalibai 879 ne hukumar kula da dalibai masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta aika jihar Barno domin yi wa kasa hidima wannan shekaran.

Jami’ar hulda da jama’a na hukumar dake jihar Barno Sadiya Yahaya ta sanar da haka a wata takarda da aka raba wa manema labarai a garin Maiduguri.

Sadiya ta ce bisa ga bayanin da kodinatan hukumar Rabiu Aminu ya yi ya ce wannan karo rukunin C, zubi na biyu ne suka yi rajista a sansanin horas da dalibai na jihar Barno dake Babbar Ruga a jihar Katsina.

Daga cikin wadanda suka yi rajista akwai maza 459 da mata 420.

Aminu ya yi kira ga masu yi wa kasa hidima da su maida hankali wajen saka ido kan abubuwan da za a koya musu a lokacin aikin bautar kasar.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta tallafa musu da motoci aiki, sannan a gina karin dakunan kwana da kuma kokarin biyan su alawus akan lokaci.

Bayan haka Aminu yace a wannan shekara jihar Barno ta samu karin yawan daliban da za su yi wa kasa hidima a dalilin zaman lafiya da aka samu.

Gwamnan jihar Babagana Zulum ya yi kira ga masu yi wa kasa hidima da su zama abin koyi ga sauran mutane ta hanyar nuna kishin kasa a ayyukan su.

Share.

game da Author