Mai Shari’a Ibrahim Shabafu ya garkame mai adawa da Gwamna Abubakar Bello na Jihar Neja a kurkukun Minna, ba tare da amincewa da beli ba.
An tura tsohon kwamishina Abubakar Katcha kurkuku a ranar 24 Ga Disamba, bayan wani mai suna Isa Lapeni ya kai karar sa a ofishin ‘yan sanda a Minna, inda ya yi korafin cewa ya kira shi a waya ya rika surfa masa zagi.
Jami’an ‘yan sanda sun gayyaci Katcha inda ya kai kan sa da kan sa. Sai dai kuma aka je kotu, inda mai shari’a ya tuhume shi da laifin cin zarafin wani dan Jihar Neja.
Lauyoyin sa sun nemi beli, amma alkali ya hana, ya ce sai an dawo kotu ranar 6 Ga Disamba, 2020.
PREMIUM TIMES ta gano cewa Gwamna Bello ya kai rahoton korafi ga jami’an ‘yan sanda, makonni uku baya, inda ya ce Katcha ya caccake shi, tare da shiga Facebook din sa ya ce gwamnan ya wawuri wasu makudan kudade.
Dukkan su dai Gwamna Bello da Katcha, a baya abokai ne, kuma sun yi kwamishina a lokaci daya a baya. A yanzu kuma su biyun duk ‘yan jam’iyyar APC ne.
Katcha a yanzu mamba ne na Hukumar Gudanarwar Hukumar Tace Finafinai ta Kasa (NFVCB).
Wani kanin sa mai suna Abubakar Katcha ya ce babu wata barazana da gwamna Bello zai yi daga hana masu adawa da shi su rika bayyana ra’ayin su.
Kakakin ‘Yan Sandan Minna, Abubakar Dan-Inna ya ce ana tuhumar Katcha da laifin cin mutuncin wani.
Tun bayan hawan gwamnatin APC a 2015 ake zargin ta da laifin danne ‘yancin masu yada labarai da kuma masu ra’ayin sukar gwamnati.
Discussion about this post