Sakamakon binciken da kungiyar kiwon lafiya ta duniya ta gudanar a shekarar 2018 ya nuna cewa Najeriya na da kashi 25 cikin kason adadin yawan mutanen dake dauke da zazzabin cizon sauro a duniya.
Binciken ya nuna cewa tsakanin shekarar 2014 da 2018 an samu raguwar yaduwar cutar a kasashen Nahiyar Afrika.
A 2017 mutane miliyan 231 aka tabbatar suna dauke da wannan cuta, sai dai kuma wannan adadi ya ragu zuwa mutane miliyan 228 a 2018.
Hakan na da nasaba ne da wayar wa mutane kai da aka yi na sanin mahimmancin kwana cikin gidan sauro da samar da ingantattun magungunan cutar musamman ga mata masu ciki da yara kanana.
WHO ta ce akwai sauran aiki da dama da ya kamata a yi musamma wanda ya shafi samarda isassun kudade domin kawar da cutar.
Da yake tofa albarkacin bakin sa game da ghaka shugaban WHO Tedros Ghebreyesus yayi kira da a maida hankali wajen sam wa mata da yara karaiya game da wannan cuta muddun ana so a samu ci gaba a kasar nan.
“Karfin garkuwan mace kan ragu da zaran ta dauki ciki da hakan ya zama dole a samar mata da magungunan da zai kare ta daga kamuwa da irin wannan cututtuka.
“Sai da bisa binciken da muka gudanar mun gano cewa mata masu ciki kalilan ne suka iya gai wa ga maganin zazzabin cizon sauro a kasashen Afrika. A dalilin haka an rika samun mata da dama na rasuwa da jarirai musamman a kasashen da suka tasowa.
Discussion about this post