Gwamnatin Tarayya ta bayyana dalilin jinkirin da aka samu na biyan kudaden alawus din N-Power har na tsawon watanni biyu.
A da dai Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ke kula da hakkin raba kudin N-Power. Amma yanzu kuma an maida tsarin a karkashin Ofishin Ministar Ayyukan Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Farouq.
A wani taron manema labarai da ministar ta yi, ta danganta laifin rashin biyan kudaden da wuri ga jinkirin damka mata ayyukan daga Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa da ta ce ba a yi da wuri ba.
Ta ce amma a yanzu ma’aikatar ta na tuntubar shugabannin bangarorin NSIP domin karasa tantancewa, kuma ana ci gaba da aikin damka wa ma’aikatar ta wannan aiki na N-Power din.
Sannan ta kara da cewa ci gaba da aiki da wadanda ake biyan alawus din N-Power, maimakon a sallame su tunda wa’adin su ya wuce, sai acdauki wasu, shi ma ya haifar da jinkirin biyan kudaden.
“ Wadanda aka dauka aikin N-Power tun cikin 2016, su na nan ana biyan su, duk kuwa da cewa tun watanni 16 da suka gabata wa’adin su ya kare.”
Sai dai kuma duk da wannan jinkiri da aka samu, Minista Sadiya ta ce ma’aikatar ta za ta samar da wata hanyar da za a biya kudaden ga masu hakkin karba da zarar an kammala karbar akalar aikin daga Ofishin Mataimakin Shugaban Kasa.
Tsarin N-Power dai tsari ne na rage wa matasa zaman-kashe-wando, ta hanyar daukar masu digiri aikin da ban a dindindin ba, ana biyan su aikin koyarwa naira 30,000 a kowane wata.