MUZGUNA WA KIRISTOCI A NAJERIYA: Sultan ya maida wa CAN martani

0

Sarkin musulmi Sultan Abubakar Saad ya nuna takaicinsa bisa bayanan da kungiyar kiristocin Najeriya tayi cewa wai musulmaina muzguna wa kiristoci a Najeriya.

Sultan ya ce bai dace ba a ce wai CAN ta na irin wadannan maganganu a kasar nan.

Bayan haka ya bayyana cewa ko koke koken da ake yi cewa wai Fulani na kashe mutane a wasu yankunan kasar nan lallai a sani cewa wannan fadace-fadace ba na addini bane.

Idan har akwai maganar muzgunawa yakamata ace CAN ta kawo wannan magana teburin ganawa da muke yi a tsakanin mu a lokutta da dama domin a san abin da za ayi akai amma ba yin irin wannan maganganu ba saboda Amurka ta ce haka a rahoton ta.

Kasar Amurka ta bayyana a rahoton ta cewa Najeriya na daga cikin kasashen duniya da ake muzguna wa kiristoci.

Kungiyar CAN ta amince da wannan rahoto inda ta jaddada cewa lallai ana muzguna wa Kiristoci a kasar nan.

Sakataren kungiyar wanda ya fitar da sakon kungiyar CAN ya ce ana ci zarafin kiristoci a jihohi kamar su Kaduna, Adamawa, Taraba da jihar Filato duk da cewa kungiyar ta tabbatar ba kiristoci ba ne kawai aka kashe a hare-hare da suke aukuwa a wadannan jihohi.

Sultan ya bayyana haka a taron kungiyar Dalibai musulmai na jami’ar Bayero da ke Kano.

Share.

game da Author