Muna rokon Buhari da kungiyar CAN su ceto mu daga Boko Haram – Malamin Makaranta

0

Daya daga cikin mutane 10 da Boko Haram suka yi garkuwa da a jihar Yobe kuma malamin makaranta ya yi kira ga shugaba Buhari da ya gaggauta ceto su daga hannun Boko Haram.

Bitrus Bwala wadda malamin makaranta ne ya bayyana cewa suna tsare a hannun Boko Haram dukkan su.

” A hanyar zuwa wurin aiki na ne ranar 27 ga watan Nuwamba Boko Haram suka yi Garkuwa da ni tare da wasu mutane.

” Dukkan mu mabiya addinin kirista ne, kuma duk muna tsare a hannun Boko Haram. Muna rokon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da shugaban kungiyar CAN su saka baki akan wannan abu, mu samu mu koma ga iyalan mu.

” A gaban mu aka kashe ma’aikatan jin kai na Kungiyar ‘AAH’ a dalilin haka muke kira da a gaggauta saka baki domin a ceto mu.

” Ko da suka kaimu maboyar su mun gamu da ma’aikatan Kungiyar jinkai da suka yi garkuwa da su, amma kuma muna gani kiri-kiri a idanun mu suka kashe su.

Bwala ya tabbatar da cewa sun gamu da daliban makaranta, Leah Sharibu dake tsare a hannun Boko Haram.

Wannan sako yana kunshe ne wani bidiyo da Boko Haram suka yada inda suka tara wadannan mutane da suka yi garkuwa da, shi kuma Bwala ya yi wannan bayanai a gaban Boko Haram din.

Share.

game da Author