Akalla sojojin Jamhuriyar Nijar 67 aka kashe a wani mummunan harin da ‘yan ta’adda suka kai musu, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya tabbatar.
Haka Buhari ya bayyana a lokacin da ya ke yin tir da wannan mummunan hari na ta’addanci, a Nijar, kasar da ke makautaka da Najariya.
Buhari ya kara da cewa an kuma kashe wasu mutane farar hula 34 a dai wannan hari da ya yi muni matuka.
A sanarwar da aka fitar jiya Laraba, wadda ya yi tir da harin wanda aka kai kusa kan iyakar Mali da Nijar, Buhari ya nuna damuwa da tashin hankali matuka.
Buhari ya nuna rashin jin dadin jin yadda maharani suka tsallako daga Mali suka kai wannan mummunan hari.
Ya nuna cewa shi da al’ummar Najeriya su na bayan Nijar dangane da wannan ibtila’i da ya samu kasar baki daya.
Ya ce Najeriya za ta ci gaba da hada kai da dukkan kasashen da ke yankin Sahel domin ganin an kakkabe ta’addanci da ‘yan ta’adda a yankin gaba daya.
Sannan kuma ya mika ta’aziyya tare da addu’ar kada Allah ya mamaita da kuma neman hanyoyin shawo kan wannan ta’addanci ta hanyar hada kai tsakanin dukkan kasashen da wannan fitina ta shafa.
‘Yan ta’adda na ci gaba da tayar da kayar baya a yankin Area maso gabcin Najeriya, a jihohin Barno da Yobe, da kasar jamhuriyar Nijar da kuma Mali.
Shekara goma kenan Najeriya na fama da hare-haren Boko Haram.
Wannan hare-hare ya fantsama har a jamhuriyar Nijar, inda kasashen biyu ke asarar sojoji, fararen hula, dukiya da kuma muhalli.