Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai
Assalamu Alaikum
Biyo bayan sanarwa da ta gabata daga “Masarautar Bichi” ta jihar Kano bisa tsige wasu hakimai guda biyar (wai da ke karkashin Masarautar kamar yadda sabuwar dokar Sarakunan jihar ta tanada) bisa rashin yiwa “Sarkin Bichi” mubaya’a.
Daga cikin hakiman akwai Sarkin Bai – Hakimin Dambatta, Alhaji Mukhtar Adnan (Shugaban Kabilar Dambazawa) wanda a kansa za mu dan yi duba cikin tarihi na kafuwar daular Usmaniyya ta jihar Kano, da ake nema a ruguza, a daidaita, saboda son zuciyar wasu.
Muhimman abubuwa game da Sarkin Bai, Alhaji Mukhtar Adnan da ya nada marigayi Ado Bayero, dansa Aminu Ado Bayero ya warware wa nadi, Daga Imam Murtadha Muhammad
1. Sakataren Majalisar masu nadin Sarakunan Kano.
2. Kwimishinan Ilimi na farko a jihar Kano.
3. Tsohon dan Majalisa, kuma tsohon bulaliyar Majalisar tarayyar Najeriya.
4. Sunan sa ne sanye a makarantar Sakandire ta Day Science College Kano.
Alhaji Mukhtar Adnan ya zama dan majalisa mai nadin Sarkin Kano a shekarar 1954, inda bayan shekaru 9 suka nada Marigayi Dr. Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano a 1963.
Sarkin Bai, shine shugaban kabilar Dambazawa, wadanda tarihi ya nuna sun taimakawa Shehu Usmanu wurin yake-yaken jihadin da aka dauki shekaru ana fafatawa.
Dambazawa sun taimaka wa Shehu Dan Fodiyo ta hanyar samar da dakarun yaki a garin Dambatta, tare da yin tsare tsaren yakin.
Bayan da Shehu Dan Fodiyo ya ci garin Kano da yaki, an shafe shekaru uku daga shekarar 1806 zuwa 1807 babu Sarki a jihar Kano, inda jagororin jihadi guda biyar suke rike da mulkin Kano.
Jagororin sun fito daga kabilun Sullubawa (Malam Jamo), Yolawa (Malam Jibir), Jobawa (Malam Bakatsine), Hausa (Malam Usman Bahaushe) da Dambazawa (Malam Muhammadu Dabo).
Kasancewar goyon baya da taimakon da wadannan kabilu suka yi wurin yin jihadin Shehu Usmanu, yasa suka kasance masu nadin Sarki, wanda daga bisani har ta kai ga Malam Dabo na kabilar Dambazawa da suke Sarkin Bai ya zama Sarkin Kano bayan kin amincewarsa da mulkin Sarki Modibbo Sulaiman na kabilar Mundubawa.
Dalilin da yasa taba Sarkin Bai ya zama taba Shehu Usmanu,
Kasancewar mutanen kabilar Dambazawa (Inda Sarkin bai ya fito) Fulani ne, jagoransu a wannan lokaci da na sauran kabilun Fulani suka je wurin Shehu domin yin karatu a wurin sa, wanda har yakin da Shehu yayi a Gudu ya riske su.
Bayan dawowar shugaban Kabilar Dambazawa, Modibbo Muhammad Yunusa (Dabon Dambazau) ya hada kan mutane domin bin shugabancin Shehu Usmanu. (Tun asalin su dama Musulmai ne).
Wanda suka zama manyan jigogin yaki da Shehu Usmanu yayi da Kano wanda har ya samu nasarar cinye garin Kano.
Bayan yaki da shekara uku, Shehu Usman bai nada Sarkin Kano ba sai dai jagororin Fulanin Kano guda biyar wanda daga ciki har da Sarkin Bai ne suke rike da madafun ikon Kano.
A wata mujallar tarihi mai taken “The Fulani Empire of Sokoto” ta tabbatar da mubaya’ar kabilar Dambazawa ga Shehu Dan Fodiyo tun kafin ya yaki Sarkin Gobir a shekarar 1802 zuwa 1808.
Kasancewar Kabilar Dambazawa a garin Dambatta suke, yasa suke rike da Hakimcin garin Dambatta da Makoda kuma ake wa sarautar lakabi da Sarkin Bai.
Kabilar Dambazawa sun kasance masu yawo daga gari zuwa gari suyi yado har ma duk inda suka zauna suke kiransa da Dambazau, wanda a yau akwai shi a garuruwan Bauchi, Kano, Katsina, Sokoto da Taraba.
Jama’ah wannan kadan kenan daga wannan tarihin mai albarka. Amma yau an wayi gari idan muna fadawa mutane gaskiya, cewa mutanen nan fa wallahi so suke yi su rusa muna addini da tarihi, wai har wasu suke kokarin musun hakan. To alhamdulillahi, gashi nan dai ta fara tabbata a fili karara. Wadannan mahaukatan ‘yan siyasar idan ba muyi hankali ba sai fir’aunancin su ya shafi kowa. Idan kuwa kuna musu, to sai in ce, Allah ya bamu rai da lafiya da nisan kwana, amin.
Wassalamu Alaikum
Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi Najeriya. 08038289761.