Ministan Makamashi, Sale Mamman ya dakatar da Shugabar Hukumar Samar da Lantarki a Yankunan Karkaka, Damilola Ogunbiyi.
Kakakin Yada Labarai na ministan, mai suna Aaron Artimas ne ya sanar da haka a yau Talata a Abuja.
Artimas ya bayyana cewa minista ya tasa keyar Damilola zuwa gida domin fara hutun dole na dakatarwa, saboda wani hardadden kullin da ake son kwancewa a hukumar da ta ke shugabanta.
An umarci Ogunbiyi ta mika mulki ga babban jami’i mafi girman mukami bayan ta.
“Daga nan kuma sai Minista Mamman ya bada umarnin a gaggauta gudanar da binciken al’amurran Hukumar Samar da Haske Lantarki a Karkara, domin sauya mata fasalin yadda za ta rika gudanar da ayyukan samar da hasken lantarki a karkara, kamar yadda aka kafa ta domin ya samar.
Shekara da shekaru kauyuka da yankunan karkara na fama da hasken lantarki. Birane ma ba a bar su a sahun bayaba wajen fama da matsalar wutar lantarki.
Dukkan alkawurran da gwamnatin Buhari ta yi na wadatar da wutar lantarki tun cikin 2015, bai samu nasara sosai ba.
Har yanzu kuma batun kafa cibiyar samar da hasken lantarki ta Mambilla Hydro Power, ya na kasa ya na dabo, ganin cewa har yanzu ba a gama karkarewa da kamfanonin da ake so su zuba jarin gudanar da gagarimin aikin kafa cibiyar ba.
Sai dai kuma duk da an dakatar da Ogunbiyi, har yau Minista Sale Mamman bai fito ya bayyana takamaimen laifin da ake zargin ta da aikatawa ba.
Discussion about this post