Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya aika da sunayen sabbin kwamishinonin sa 19 majalisa domin tantance su.
Matawalle ya mika wannan sunaye ne ranar Talata wanda Kakakin majalisar Nasiru Magarya, ya shaida wa ‘yan uwansa a zauren majalisar.
Sannan kuma da masu bada shawara 28.
Wadanda aka tura sunayen su sun hada da:
Sulaiman Tunau, Aminu Sulaiman, Abdulkadir Gora, Jinaidu Muhammad, Muhammad Maiturare, Zainab Gummi, Jamilu Aliyu, Nura Isah, Rabiu Garba, Sufyanu Yuguda, Ibrahim Magayaki, Yahaya Gora, Yahaya Kanoma, Tukur Jangebe, Ibrahim Mayana, Abubakar Tsafe, Nura Zarumi, Bilyaminu Shinkafi da Abubakar Muhammad.