MANJO JANAR MUHAMMDU BUHARI: Fadar Shugaban Kasa ta yi wa jaridar PUNCH raddi

0

Fadar Shugaban Kasa ta fitar da sanarwar yin raddi ga jaridar PUNCH, wadda ta buga zazzafan ra’ayin ta da kuma matsayar da ta ce ta cimma, dangane da irin salon mulkin kama-karya da ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ke tafiyarwa a Najeriya.

A cikin ra’ayin da PUNCH ta buga yau Laraba, ta ce Buhari yay i kaurin suna wajen take umarnin kotu, tun bayan hawan sa mulki cikin 2015 zuwa yau.

Cikin misalan da PUNCH ta bayar, har da yadda aka take umarnin kotu wajen cin zarfin Omoyele Sowore.

Sunan rubutun da PUNCH ta yi wa Buhari shi ne, “Matsayin Mu Dangane da Rashin Bin Doka da Oda Da Buhari Ke Yi.”

PUNCH ta ce, “ Ba za mu sake kiran Buhari da sunan Shugaban Kasa ba, sai dai mu kira shi da sunan san a ainihi, a lokacin da yayi mulkin soja, wato Manjor Janar Muhammadu Buhari (ritaya).”

Jaridar ta ce wannan sunan ne ya fi dacewa da shi, domin duk da cewa mulkin dimokradiyya aka zabe shi ya gudanar, amma kuma mulkin sa daidai ya ke da irin na tirsasawa da kama-karya, kamar yadda yay i a lokacin da yay i shugabancin mulkin soja.

Sai dai kuma wannan matsaya da jaridar PUNCH ta dauka, ta sa Fadar Shugaban Kasa yin gaggawar maida martani, ta bakin Kakakin Shugaban Kasa, Femi Adesina, wanda ya bayyana cewa, “matsayar da PUNCH ta dauka ta kara tabbatar da cewa akwai ‘yancin fadar albarkacin baki a karkashin mulkin Buhari.”

Sanarwar da Fadar Shugaban Kasa ta bakin Adesina ta fitar, ta ce, jaridar ta ce daga yau za ta ci gaba da kiran Shugaba Muhammadu Buhari da mukamin san a soja, wato Manjo Janar.

“To ai wannan ba wani abu ba ne, domin mukami ne da Shugaban Kasa ya samu bayan namijin kokari da kishin da ya nuna wajen bauta wa kasar nan, kafin ya yi ritaya. Kuma a yau, dokar kasa ta ce shi ne Babban Kwamandan Sojojin Najeriya.

“A duk duniya, ba nan kasar kadai ba, Janar-Janar na soja masu dimbin yawa sun rungumi dimokradiyya. Hakan kuwa bai nuna cewa wadanda ba su yi aikin soja sun fi su nagarta ba.

“Kenan wanda ya ce zai rika kiran sa da mukamin san a soja, wata alama ce da ke tabbatar da akwai ‘yancin fadar albarkacin baki da ‘yancin ‘yan jarida, wanda wannan gwamnati, ko wannan mulkin kama-karya, kamar yadda duk wanda ya ga dama zai kira gwamnatin ta jaddada cewa za ta kare da mutuntawa.’’

Share.

game da Author