Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle yayi kira ga malaman jihar da mutane da su zurfafa yin addu’o’i domin tona asirin wadanda suka la’anta alkurani a jihar.
Matawalla ya yi wannan kira ne a wajen taron gasar karatun Alkur’ani da aka yi a jihar Zamfara.
Ya kara da cewa muddun ba a dage da addu’o’i ba to fa jihar za ta iya gamuwa da fushin Allah domin la’anta Alkurani da abin wasa bane,
“Gwamnati ta nada kwamiti domin yin bincike game da wannan mummunar abu da aka aikata a jihar. Sannan kuma ina so in shaida wa jama’a cewa ba za mu zuba ido ana yin irin wannan iya-shegen a jihar mu ba da ya kai ga bai tsaya ga mutaen ba har Kur’ani ana ci wa mutunci.
Sannan kuma ya yaba wa wadanda suka shirya wannan taro yana mai cewa gwamnati za ta mara musu baya matuka domin samun nasara a gasar.
” Wannan gasa shine zai zabo mana hafizai gogaggo masana Karatun Alkur’ani da zasu wakilcemu a Kasar Karatu ta Kasa da za a yi a shekara mai zuwa.
A kwanakin baya gwamnati ta taba yin kira da mutane su ta shi da azumin kwanaki uku domin rokon Allah ya tozarta sannan ya tona wadanada suk la’anta kur;ani a jihar. An dai wayi gari ne aka ga fallayen Alkurani a kwataci da lambatu an yi kaca-kaca da su.
Matawalle ya yi kira ga limamai a duk masallatan jihar da su yi addu’o’I na musamman tare da yin wa’azi domin tunatar da mutane laifin yin haka.