Majalisar Tarayya ta nemi a hana motar da ba ta da fentin taksi yin haya a Abuja

0

Watanni biyu bayan da Hukumar Babban Birnin Tarayya ta fatattaki masu Keke NAPEP daga Abuja, yanzu kuma mambobin Majalisar Tarayya sun yi kira ga hukumar ta FCT da Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) su gaggauta haramta duk wata motar hayar da ba ta da fentin taksi daukar fasinja a cikin Abuja.

Sannan kuma Majalisar Tarayya har yau ta nemi a hana duk direban da ba shi da lasisi yin tuki a babban birnin na tarayya.

Daga nan kuma sai majalisa ta umarci hukumar zirga-zirgar sufuri ta gaggauta yi wa dukkan motocin da ke Abuja rajista da kuma tilasta kowa ya mallaki tasisin tuki.

Sun ce wannan doka za ta hau kan gaba daya masu motocin haya da kuma masu motocin da ban a haya ba.
Dan Majalisar Tarayya Leke Abejide ne ya gabatar da wannan kudiri, ganin yadda Abuja ta cika makil da motocin da bas u da fentin taksi kuma ana haya da su.

Ya ce wannan yawaitar haya da motocin da bas u da fentin taksi ya haifar da yawaitat satar mutane da yi musu fashi da yin garkuwa da su a cikin Abuja da kewaye.

“A dukkan biranen kasashen da suka ci gaba, kafin a fara haya da mota sai an yi mata rajistar yin haya da ita, sai an yanki lasi, sai kuma an yi mata fentin taksi, sannan kuma an mai tuka motar ya yanki takardar izni. Kuma sai kamfani ami rajista ne kadai zai yi harkar motocin haya.” Cewar Abadije.

Dokokin Tukin Da Aka Kasa Yin Amfani Da Su A Abuja

Idan ba a manta ba, tun farkon shekarar 2018 ce Sakataren Kula da Sufuri da Zirga-zirga na Hukumar Babban Birnin Trayya, Abuja, ya fito da wasu sabbin ka’idojin tukin motocin haya masu daukar fasinja a Abuja.

Kayode Opeifa, ya ce ma’aikatar sa ta fito da ka’idojin bayan wani taro da ta yi da direbobin taksi.

Ka’ida ta farko ita ce, dukkan manyan motocin haya, bas-bas, taksi, Keke-NAPEP da baburan acaba masu haya a garuruwan kewayen Abuja ko cikin Abuja, to tilas su kasance dauke da jar lambar mota, maimakon ruwan bula wacce sun san ba ita ce lambar motocin haya ba.

“Sannan kuma duk wata motar haya da ake haya da ita a Abuja, to ya kasance ta na dauke ne da lambar Abuja, daga I Ga Oktoba, 2018.

“Duk taksi da za a yi haya da ita a Anuja, to ya kasance ta na da na’urar sanyaya jiki da mota, wato air condition kafin nan da ranar 1 Ga Oktoba, 2018.
“Duk motocin haya da ke Abuja su kasance su na dauke da takardun shaidar cancantar ingancin amincewa a yi haya da su. Za su mallaki kwafi biyu na wannan takardar shaida daga ofishin bada iznin cancantar da ke Abuja.

Opeifa ya kara da cewa kowane direban motar haya ya kasance ya na da gangariyar lasisin tuki, wanda bayan ya mallake shi, sai ya je sakateriyar Hukumar FCT sun sake tabbatar da sahihancin sa.

Ya kara da cewa kowane direban motar haya tilas ya rika mallakar takardar biyan haraji a Abuja.

An kuma yarda duk wanda ya cika wadannan sharudda ya rika dauka da ajiye fasinja a Abuja, matsawar dai inda aka amince masa ya tsaya ya ajiye ne, ko kuma wurin da doka ta ce ya tsaya ya dauki fasinja.

Laifi ne babba direban motar haya a tsaya inda zai takura wa motoci masu wucewa ko masu gilmawa.

Direbobin Keke-NAPEP su tabbatar da sun rika bi hanyoyin da doka ta ce su rika bi kawai.

Masu Keke-NAPEP da masu baburan acaba ba a yarda su yi haya da ababen hawan da Hukumar Abuja ba ta ba su tambarin shaidar iznin aiki a Abuja da kewaye ba.

Dukkanin masu manyan motocin haya, bas-bas, taksi, Keke-NAPEP, su garzaya ofishin da za a yi musu rajistar kididdigewa a bayar da iznin haya a Babban Birnin Tarayya da kewaye.

An dakatar da bada lasisin iznin yin haya a Abuja, har sai yadda hali ya yi.

Daga yau an hana kungiyoyin direbobin haya da manyan motoci, taksi, Keke-NAPEP da baburan acaba su yi wa wani rajistar zama mamba a cikin su.

Sakateriyar Hukumar Babban Birnin Tarayya na bukatar dukkan masu kamfanonin motocin haya da ke aiki a karkashin kafanoni su kai jerin yawa da lambobin adadin motocin da ke haya a karkashin kamfanonin su, kafin nan da ranar 13 Ga Afrilu, 2018.

Sai dai kuma sama da shekara daya kenan har yau ba a yi amfani da wadannan dokokin ba.

Korar da aka yi wa masu Keke NAPEP watanni biyu da suka gabata daga Abuja, ta haifar da cunkoson motocin haya kwararrababbu, wadanda ke bin hanyoyin da aka hana masu Keke NAPEP zirga-zirga.

A yanzu Abuja cike ta ke makil da tsoffin motocin da kamata ya yi a ce an jefar da kwangwanayen kangarwar motocin a Kwakwacin tsoffin motoci.

Share.

game da Author