Majalisar Kano ta amince da kirkiro sabbin masarautu hudu

0

Majalisar dokokin jihar Kano ta rattaba hannu a kudirin kirkiro sabbin masarautu a jihar Kano.

A bisa wannan doka da aka amince da, za a kirkiro da sabbin masarautu hudu sannan kuma za su rika canjin shugabanci duk bayan shekara biyu.

Shuagaban masu rijaye na majalisar dokokin jihar Abdul-Madari,ya bayyana cewa majalisar ta amince a kirkiro wannan masarautu ne saboda ci gaban jihar.

Majalisar ta gaggauta amincewa da kudirin ranar Alhamis domin gwamnatin Ganduje ta samu damar kirkiro wannan masarautu.

Idan ba a manta ba a karo na biyu, gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya sake aikawa da kudirin kirkiro sabbin masarautu hudu a jihar zuwa majalisar dokokin jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Muhammad Garba, ne ya sanar da haka a wata takarda da ya raba wa manema labarai.

Garba ya ce tun bayan kotu ta soke sabbin masarautun a bisa wasu dalilai da ta ce ba a yi daidai ba a kan su, gwamnati ta sake zama domin sake aika wa da kudirin kirkiro da sabbin masarautun sannan a yau Litinin, ta aika wa majalisar Jihar.

Hakan ya biyo bayan rusa masarautun ne da kotu tayi ne a bisa dalilin cewa ba a kirkiro su bisa ka’ida ba.

” Ina so ku sani cewa, wasu masarautun da aka kirkkiro sun fi masarautar Kano asali da dadadden tarihi. Sun kafu tun kafin masarautar Kano. Wannan yana daga cikin dalilan da ya sa muke so mu dawo wa wadannan masarautu ikon su da martaba.

” An taba kokarin kirkiro irin wadannan masarautu amma ba su dore ba, a yanzu gwamnatin Ganduje na so ta ga hakan ya tabbata sannan sun tsayu gidigam.

Garba ya ce bayan haka anyi gyara ga dokar d masarautun Kano domin kawo ci gaba a jihar ne sannan ya yi kira ga majalisar dokokin jihar da su gaggauta kammala aiki a kai domin ba gwamnati damar kirkiro wadannan masarautu.

Masarautun da majalisa ta amince da su sun hada da Masarautar Rano, Gaya, Bichi da Karaye.

Share.

game da Author