Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa majalisa za ta amince Shugaba Muhammadu Buhari ya sake ciwo bashin zunzurutun dala bilyan 29.96.
Da ya ke wa manema labarai karin bayani a jiya Litinin, ya ce Majalisar Dattawa za ta amince da dokar da ta halasta ciwo bashin, amma kuma za ta rika bin diggigin ayyukan da za a rika yi da kudaden.
“Za mu rika sa ido sosai, kuma za mu rika tabbatar da cewa ko sisin-kwabo ba a karkatar daga ainihin ayyukan da ya kamata a yi da kudaden ba.”
Ranar 28 Ga watan Nuwamba ne dai Shugaba Buhari ya aika wa Majalisa wasikar neman amincewa gwamnatin tarayya ta ciwo wannan bashin da ta tsara yadda za ta yi da kudaden tun a cikin 2016 zuwa 2018.
Tun a wannan lokacin Buhari ya aika wa Majalisa karkashin Bukola Saraki, cewa ta na son ciwo bashin daila bilyan 30 domin yin ayyuka daga 2016 zuwa 2018, amma ta ki amincewa, saboda akasarin mambobin majalisar sun ki amincewa a narko wannan bashi.
Abinda Za A Yi Da Kudaden Bashin -Buhari
A wannan sabuwar wasika da Buhari ya aika wa majalisa a karkashin Sanata Ahmed Lawan, ya ce idan aka ramto kudaden, za a yi ayyuka da su ne a kowane bangaren fannonin raya kasa da inganta tattalin arziki.
Musamman inji Buhari za a yi ayyukan inganta rayuwar jama’a, ayyukan noma, kiwon lafiya, ingnta ilmi, samar da ruwan sha da kuma kara samar wa jama’a ayyukan yi.
Dalilin Mu Na Kin Yarda A Ciwo Bashin Zamanin Saraki
Sai dai kuma tsohon Sanata Shenu Sani, ya bayyana cewa sun ki amincewa da a ciwo bashin a Majalisar Dattawa karkashin Bukola Saraki, saboda yin haka zai tinjima karar nan da ‘yan kasar cikin wawakekiyar rijiyar da ruwan bashi zai hadiye Najeriya gaba daya.
Shenu Sani, wanda a zamanin Saraki shi ne Shugaban Kwamitin Majalisa Mai Lura da Basussukan Cikin Gida da na Waje, y ace a baya sun ki amincewa da ciwo bashin, domin yin haka, zai sake maida Najeriya a hannun ‘yan mulkin mallakar da za a rika tatse tattalin arzikin mu ana mika musu, saboda tsananin bashin da suke bin kasar nan.
Adadin Bashin Da Buhari Ya Gada Da Wanda Ya Ciwo
Lokacin da Buhari yah au mulki, ya zuwa karshen 2015 ana bin Najeriya bashin dala bilyan 10.32. Amma kuma zuwa watan Yuni na 2019, ana bin Najeriya bashin dal bilyan 22.08, wato wanda Buhari ya ciwo har ma ya nunka wanda ya gada kenan, kuma yah aura.
Wannan ya na nufin da Majalisar Dattawa lokacin su Saraki da Shenu Sani ta amince Buhari ya ciwo bashin dala bilyan 30 da ta ki amincewa, da yanzu ana bin Najeriya bashin dala bilyan 52 kenan.
Yanzu dai kamar yadda Sanata Lawan ya fadi, Majalisa za ta amince wa Buhari kara ciwo wannan bashi. Wannan kuwa abu ne mai saurki, domin APC ta fi rinjaye a cikin majaliasar.