Mahara sun kashe mutane biyu a jihar Adamawa

0

Mahara dauke da muggan makamai sun kai hari kauyen Holma dake karamar hukumar Hong jihar Adamawa inda suka kashe mutane biyu sannan daya ya tsira da rauni a jikin sa.

Mazaunan kauyen Holma sun ce maharan sun bankawa gidaje sama da 20 da kayan abinci wuta.

Sun kara da cewa an fara samun zaman lafiya a kauyen a dalilin zuwan jami’an tsaro na sojoji, ‘yan sanda da Sibul Difens.

Shugaban karamar hukumar Hong Usman Waganda da ya ziyarci kauyen kuma ya bayyana cewa gwamnati da jami’an tsaro ba za su yi kasa-kasa ba wajen ganin sun kamo wadannan mahara da suka aikata wannan mummunar abu.

” Ina kira ga mutanen wannan kauye da su rika ankare wa, kuma yana da kyau a kafa kungiyar sa kai domin samar da tsaro a jihar saboda kauce wa irin haka. Yin haka zai taimakawa jami’an tsaro wajen farautar ire-iren wadannan bata gari.

A bayanin da ya yi dagacin kauyen Holma Michael Wayamomni yace maharan sun far wa kauyen su ne da karfe 11 na daren Lahadi.

Wayamomni ya kara da cewa maharan sun shigo suna barin wuta ta ko ina da hakan yayi sanadiyyar rasuwar mutane biyu nan take sannan wani yaji rauni a jikin sa. ” Sannan Kuma sun sace mana shanu uku.”

Wayamomni ya yi kira ga gwamnati da jami’an tsaro da su gaggauta samar wa kauyen da tsaro domin gujewa aukuwar irin haka.

Shima kakakin ‘yan sandan jihar Suleiman Nguroje ya tabbatar da aukuwar wannan al’amari.

Share.

game da Author