A ci gaba da aikawa da gudunmuwa da ‘yan Najeriya suke ta yi don tallafawa fitattcciyar mawakiyar Hausa Magajiya Dambatta wanda Jaafar Jaafar da wasu aminan sa da suka hada da Musa Abdullahi Sufi, Ibrahim Sanyi-Sanyi da Ibrahim Musa suka kaddamar, ‘yan Najeriya na ta aikawa da na su gudunmuwar
Fitaccen dan jarida Jaafar Jaafar ne ya bude wannan asusu tare da hadin guiwar wasu abokan sa domin taimakawa mawakiya Magajiya Dambatta.
Tun bayan da Jaafar ya saka wakar ta a shafinsa ta Facebook sannan kuma ya ziyarce ta har gida a garin Dambatta, abinda ya gani ya bashi tausayi ga wannan mawakiya.
Kamar yadda ya rubuta a shafin sa sannan ya saka bidiyon ziyarar, ya iske Magajiya ta na bara domin ta samu abinci da abinda da za ta saka.
Bayan haka ta makance a dalilin rashin kula da bata samu.
Wannan kokari da Jaafar da abokan sa suka yi ya samu yabo da jinjinawa daga mutanen Najeriya.
Ire-iren wadannan mutane suna da dimbin yawa a arewacin Najeriya da aka yi watsi da su.
Idan ka zo garin Kaduna da Kano, zaka ga fitattun ‘yan wasa na da da suka raya arewa da al’adunta amma kuma wasunsu hatta kudin asibiti ma basu da shi ballantana na karin kumallo.
Babu wani tanadi da gwamnati kokuma gwamnatocin Arewa suka yi domin taimakawa wadannan jarumai.
Jarumai da suka rika fitowa a shirye shirye kamar su, Tumbin Giwa, Karkuzu na bodara Ikon Allah, Gidan Kashe Ahu, Ba’are, Dan wanzam, Goloko, Samanja Mazan Fama, Kasagi Na Halima, da Magana Jari Ce da dai sauransu duk wasun su na nan cikin kangin talauci da rashin lafiya.
Ya kamata a kirkiro irin wannan asusu domin taimakawa mutane irin haka musamman idan aka yi la’akari da irin gudunmuwar da suka ba yankin Arewa wajen inganta tarbiyya, auratayya, hadin kai da cigaban kasa.
Dole ne kungiyan gwamnonin Arewa su su karkato da akalarsu wajen koyi da irin wannan himma na da Jaafar Jaafar yayi wajen bude asusu domin ire-iren wadannan fitattun ‘yan arewa arika tallafa musu koda sau daya ne ko sau biyu a shekara.
Idan gwamnoni, da shufabannin kasa da suka wuce suna samun irin wannan tallafi suma mawakan mu na da da jaruman wasan kwaikwayo na bukatar a basu irin wannan kula.
Har yanzu dai za a iya saka gudunmuwa a asusun tallafawa a Magijiya Danbatta kamar haka:
Ac No: 0158190874
Ac Name: Friends of the Community Organization
Bank: GTBank.