Ma’aikatar kiwon lafiya ta jihar Ogun ta sanar cewa mutane biyar sun rasu a dalilin kamuwa da cutar kwalara ko kuma cutar amai da zawo a jihar.
Babban sakataren ma’aikatar Adesanya Ayinde ya fadi haka a taron manema labarai da aka yi a Abeokuta a makon da ya gabata.
Ayinde yace cutar ta bullo ne a karamar hukumar Abeokuta ta Arewa a kayukan Kuto, Kobito, Abule-Otun, Lafenwa na cikin wuraren da aka gano cutar.
Ya ce ma’aikatar su ta samu rahotannin cewa mutane takwas sun kamu da cutar daga asibitocin dake kananan hukumomin sannan mutane hudu kuma an gano su daga wadannan kauyuka.
Kamar yadda aka sani cutar kwalara ko kuma cutar amai da zawo cuta ce dake yawan sa mutum yin bahaya da amai sannan rashin gaggauta daukan mataki kan iya yin ajalin mutum a cikin lokaci kalilan.
Sakamakon binciken kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ya nuna cewa mutane miliyan 2.9 sun kamu da cutar sannan mutane 95,000 na rasuwa a ksashe masu tasowa a dalilin wannan cuta.
Alamun kamuwa da cutar kwalara.
1. Zazzabi.
2. Amai da gudawa.
3. Rashin jin karfi a jiki.
4. Rashin iya cin abinci
5. Suma.
Hanyoyin gujewa kamuwa da cutar.
1. Tsaftace muhalli.
2. Wanke hannu da zaran an yi amfani da ban daki.
3. A guji yin bahaya a waje.
4. Amfani da tsaftattacen ruwa.
5. Wanke hannu kafin da bayan an ci abinci.
6. Cin abincin dake inganta garkuwan jiki.
7. Yin allurar rigakafi
8. Zuwa asibiti da zaran an kamu da cutar.
likitoci sun yi kira da arika gaggauta garzaya asibiti domin warkar da cutar.
Discussion about this post