Kungiyar jinkai ta AAH ta yi matukar nuna rashin jin dadinta da jimamin rasa wasu ma’aikatan ta da Boko Haram suka kashe.
AAH tace bata ji dadin yadda ta rasa wadannan ma’aikata ba, sannan kungiyar ta yi kira ga mutane da su kiyaye wajen yada hotunan wadannan aka kashe saboda
Kada a tada hankalin yan uwan wadanda suka rasu.
” Wannan kisa ya tada mana da hankali matuka. Sannan muna kira ga wannan kungiya da su saki Grace da ita ce kadai ta rage tsare a tare da su.
Idan ba a manta an ruwaito kungiyar Boko Haram ISWAP da suka yi garkuwa da wasu ma’aikatan kungiyar jinkai ta ‘Action Against Hunger’ sun kashe su.
Kungiyar basu kashe Grace Taku ba da ita ce mace daya cikin wadanda suka yi garkuwa da din.
Ahmed Salkida, fitaccen dan jarida ne ya saka bayanin kisan wadannan ma’aikata a shafinsa ta tiwita.
Kungiyar ta yi garkuwa da wadannan ma’aikata su biyar a wajen aikin agaji ga mutanen da suka tagayyara a dalilin hare-haren Boko Haram.
PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda Boko Haram din suka yi garkuwa da wadannan mutane mutane a wani harin kwantar bauna da suka yi wa motar su a watan Yuli.
Tun a watan Satumba suka kashe mutum daya Saura mutane biyar cikin wadanda suka yi garkuwa da.
Yanzu sun kashe ma’aikata hudu cikin sauran biyar din.
Mace daya kuma da ta rage sun mai da ita baiwa.