Kotu ta bada umarnin a tasa keyar Babban Fasto na Cocin Sotitobire Miracle Cnetre zuwa kurkuku, bisa zargin bacewar jariri a cikin cocin sa, wanda ake zargin sa da sace yaron.
A yau ne Kotu a Akure, babban birnin jihar Ondo, ta ce a ci gaba da tsare Fasto Alfa Babatunde a kurkukun Olokuta, saboda sace jariri mai suna Gold Kolawole da ake zargin sa a cocin sa, tun a ranar 10 Ga Nuwamba.
Kotu na tuhumar sa da hada-baki a sace jariri a cikin cocin sa.
PREMIUM TIMES ta ruwaito wannan labari a makon da ya gabata.
Kotu na zargin wani mai suna Anjorin da lalata wasu bayanai na sirri da za a iya kafa hujja da su a wurin binciken yadda aka sace jinjirin.
Jami’an SSS ne suka gurfanar da su a kotun Majistare ta Akure.
An gurfanar da Babatunde tare da wasu mutanar shida, wato Omodara Olayinka, Margaret Oyebola, Grace Ogunjobi, Egunjobi Motunrayo, Esther Kayode da kuma Peter Anjorin.
An ce a ci gaba da tsare su a kurkuku, har zuwa ranar 14 Ga Janairu, ranar da alkali zai ci gaba da shari’a.
SSS sun damke su bayan da iyayen jaririn suka shigar da korafin su a ofishin, tare da zargin cewa jami’an ‘yan sanda na neman yi wa lamarin walle-walle.
Ranar Larabar da ta gabata ne dai mafusata suka yi raga-raga tare da kone katafaren cocin kurmus a Akure.
An yi zargin an kashe jaririn aka binne gawar sa a cikin cocin, bayan an yi tsafi da shi.
Sai dai kuma jami’an ‘yan sanda sun ce ba gaskiya ba ne.