Babbar Kotun Abuja da ke Apo, ta bada umarnin a tsare wasu mambobin IMN, mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky a kurkukun Kuje da na Suleja da ke Abuja.
Mai Shari’a Sulaiman Belgore ne ya bada wannan umarni a jiya Talata, inda ya amince da rokon da lauya mai gabatar da kara, Simon Lough, wani Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda ya nemi a yi.
An dai kama mabiya Shi’a su 60 ne tun a ranar 22 Ga Yuli, a lokacin wata zanga-zanga Sakateriyar Gwamnatin Tarayya, Abuja, inda har aka ran wani Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sansa mai suna Usman Umar.
Haka nan kuma an rasa ran wani dan bautar kasa mai suna Precious Owolabi, da ake aikin horaswa a Gidan Talbijin na Channels.
Tun a ranar 27 Ga Nuwamba ne Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, FCT ta gurfanar da su, bisa zargin su da laifin haddasa mutuwar wasu, tada yamutsi da hana jama’a zaman lafiya da kuma barnata dukiyar gwamnatin tarayya.
Dukkan wadanda ake zargin dai sun karyata zargin da ake yi musu. Sun ce karya ‘yan sanda ke yi musu.
Mabiya Shi’a na ci gaba da zanga-zanga a Abuja domin nuna a saki jagoran su da kuma matar sa, wadanda ake tsare da su, tun cikin watan Disamba, 2015.
An ruwaito cewa an kashe sama da mabiyan Shi’a 340 cikin Disamba, 2015, lokacin da tankiyar da suka yi da tawagar sojoji ta yi munin da aka bude musu wuta.
Har yau dai ba a hukunta ko da jami’in soja da ba.
Da aka koma kotu a jiya Talata, lauyan wadanda ake zargin mai suna Bala Dakum, ya nemi a bada belin wadanda ake zargin.
Sai dai kuma nan take kotu ta sanar da Dakum cewa, ba beli daya tal zai rubuta nema ba, sai dai ya ruta neman belin su 60 din daban-daban, amma gaba dayan su.
Daga nan Lauya Dakum ya janye belin farko da ya nema, ya sake rubuta wani sabon belin.
Daga nan shi kuma mai shari’a sai ya soke belin, ya ce a tsare su a kurkuku.
Nan da nan mai gabatar da kara ya nemi a tsare maza 54 a kurkukun Kuje, su kuma mata su 6 a tsare su a kurkukun Suleja.
Sannan kuma ya roki kotu ta mai da shari’ar kowa a garin da aka tsare shi.
Mai Shari’a ya bada damar yi musu shari’a a Kuje.
Ya kuma dage shari’ar zuwa 5 Ga Fabrairu, 2020 domin fara shari’ar gadan-gadan, kuma ya ce za a rika gudanar da shari’a a kowace rana.
Discussion about this post