Babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’a Ahmad Tijjani Badamasi ta dakatar da gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje daga nada shugaban majalisar Sarakunan Kano, da kuma nada membobi a majalisar.
Masu nada Sarki na halal (King makers) a masarautar Kano ne dai suka shigar da kara a gaban mai shari’ar, inda suka nemi da kotu ta dakatar da gwamnan jihar Kano daga mugun shirin nasa.
Kamar yadda muka samu bayanin wannan hukunci da kotu ta yanke gwamnati za ta dakatar da wannan sabon nadi da tayi wa sarkin Kano Sanusi kenan.
Wannan shine karo na biyu da gwamna Ganduje ke shan kayi a kotu akan shari’ar masarautar Kano.
Kotu a watan Nuwamba ta dakatar da shi daga kirkiro sabbin masarautu a jihar.
Duk da cewa daga baya ya sake aikawa da wannan kudiri majalisa, kuma ta amince da ita, domin bai dauki majalisar awa daya ba wajen karantawa da amincewa da wannan kudiri ta zama doka ba.
Daga nan sai gwamna ya rattaba wa wannan kudiri hannu ta zama doka, sannan ya nada sarkin Kano shugaban majalisar sarakunan jihar.
Ya kuma umarce shi da ya gaggauta kiran mitin na wannan majalisa.
Saidai kash hakar sa da alaman ba zai cimma ruwa ba domin kotu ta sake dakatar da shi daga yin haka.
Bayan haka Imam Murtadha Muhammad da ya tattauna da mu akan haka ya yi addua ga dukka masarautun musulunci.
” Muna rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala, don tsarkin Sunayen sa, yaci gaba da kare mutuncin masarautar Kano mai daraja, mai dimbin tarihi, da daukacin dukkanin masarautun mu na Musulunci, na arewa, daga sharri da makircin miyagun ‘yan siyasa, amin.”
Idan ba a manta gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya nada Sarkin Kano shugaban majalisar sarakunan Kano.