Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a karkashin Mai Shari’a Binta Nyako, ta bayyana cewa jami’an tsaro sun tafka laifi da suka har cikin gidajen wasu mata masu zaman kan su a garuruwan da ke wajen Abuja suka kama su.
Mai Shari’a Binta Nyako ta ce laifi ne babba da jami’an su ka hakkin matan har cikin gida suka kama su, a cikin watan Fabarairu, 2017, suka zarge su da sana’ar karuwanci.
Jami’an Tsaron Tafi-da-gidan-ka na Hukumar Tsaftace Abuja, da suka hada da ‘yan sanda da sojoji ne suka yi kamen karuwan a lokacin.
Wannan hukunci da kotu ta zartas dai ya biyo bayan karar da wata Kungiyar Lauyoyi ce ta shigar, mai kare hakkin jama’a, mai suna Lawyers Act, a madadin matan da aka kama din.
Haka kuma sun hada har da Hukumar Kula da Tsatace Muhalli ta Abuja.
Wata mata mai suna Constance Nkwocha tare da wasu mata su 15 ne suka shigar da karar.
Sun kai karar ’yan sanda, sojoji da kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja,
“Shiga da aka yi har cikin gida aka kamo wadannan mata, keta musu hakki ne, kuma shiga gonar su ce. Saboda doka ta ba su damar kadaicewa a cikin gdajen su, ba tare da wani ya kutsa musu ba.” Inji Mai Sharia Zainab Nyako.
“Ita dai doka ba a kara-zube ta ke ba. Saboda ta shimfida ka’idojin da za a bi kafin a kama mutum. Don haka ya zama tilas jami’an tsaro su rika taka tsantsan, su rika bin tsarin da doka ta gindaya.”
Daga nan sai kotu ta umarci wadanda aka kai karar shiga hakkin karuwan cewa kowane ya biya kowace mata masu zaman kaln ta, Naira 100,000.
Lauya mai shigar da kara ya shaida wa kotu cewa jami’an tsaron da suka je kamen sun dirka wa karuwai satar kudaden su a gidajen da suka kamo su.
Kungiyar Kare Hakkin Matan ta ce bayan an kama su, an kwashe musu kudade sannan kuma suka gallaza musu azaba.
Discussion about this post