Ko ka amsa wasikar mu cikin kwana biyu ko, – Ganduje ga Sarki Sanusi

0

Gwamnatin jihar Kano ta ba sarkin Kano Muhammadu Sanusi kwanaki biyu ya amsa wasikar da gwamnati ta aika masa ko kuma a dauki tsatssaurar mataki a kan sa.

Babban sakataren ma’aikatar ayyukan musamman na jihar, Musa Bichi ne ya saka wa takardar hannu wadda aka mika wa sarki ranar 20 ga wata.

Bichi ya bayyana cewa Ganduje ya umarci sarkin Kano Sanusi ya gaggauta saka hannu a wannan takarda ta amincewa da nadin sa shugaban majalisar sarakunan Kano, sannan ya gayyato su duka domin zaman majalisar ta farko.

Sai dai kuma mutane da dama na ganin gwamna Ganduje yayi haka ne domin ya samu dalilin aikata wani boyayyar manufa ta sa.

Idan ba a manta ba Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa wasu gamayyar kungiyoyi 35 sun mika masa takardar kira da ya gaggauta tsige sarkin Kano Muhammadu Sanusi.

Kakakin gwamna Ganduje, Abba Anwar, ya bayyana cewa jagorar wannan kungiyoyi Komared Ibrahim Ali ne ya saka wa takardar hannu.

Kungiyoyin sun yi kira ga gwamna Ganduje ya gaggauta tsige sarkin Kano Muhammadu Sanusi.

Sun koka cewa Sarki Sanusi ya na kokarin kirkiro wata jiha a cikin Kano a bisa ire-iren ayyukan da yake yi isa da jijji da kai.

Sarki Sanusi da gwamna Ganduje sun sa kafar wando daya a dalilin rashin goyon bayansa da ake zargi sarki bai yi ba tun a zaben 2019.

Da farko dai Ganduje ya fara ne da kirkiro sabbin manyan masarautu domin rage wa Sarki Sanusi karfin iko a jihar. Daga nan aka shiga kotu. A nan ma Ganduje ya sha kasa bayan kutu ta umarce shi da a dawo yadda ake ada.

Daga nan sai Ganduje ya sake aikawa majalisar jihar sabon kudirin kirkiro sabbin masarautu hudu a jihar da hakan ya samu amincewar majalisar cikin awowi 24 Ganduje ya saka wa wannan doka hannu.

Ganduje umarci Sarkin Kano ya gayyaci duka sabbin sarakunan da aka kirkiro domin kafa sabuwar majalisar sarakunan jihar wanda Ganduje ya nada Sarki Sanusi shugaba.

Tun daga wancan lokaci da gwamnan ya umarci sarki Sanusi yayi hakan, bai yi hakan ba.

Wannan kungiya ta kara da cewa sarki Sanusi na yi wa gwamnatin Ganduje da jihar Kano zagon kasa sannan yana yi mata taurin kai ba ya bin umarninta da dokar jihar. ” A dalilin haka yasa muke kira ga gwamna Ganduje da ya gaggauta daukar mataki akai ya tsige shi kwata-kwata kowa ma ya huta kafin ya bata ruwa.

” Sannan kuma a bisa hukuncin da kotu ta yanke kan kirkiro sabbin masarautun, muna kira ga gwamna Ganduje ya gaggauta tabbatar da kirkiro wadannan masarautu kamar yadda dokar Kano bashi.

Share.

game da Author