Kasafin 2019: NHIS ta kashe Naira biliyan 15.2 daga cikin kudaden da aka ware mata- Enhaire

0

Ministan kiwon lafiya Osagie Enhaire ya bayyana cewa hukumar inshorar lafiya ta kasa (NHIS) ta kashe Naira biliyan 15.2 daga kason da aka ware wa hukumar a kasafin kudin 2019.

Enhaire ya fadi haka ne a wani taro da kwamitocin kiwon lafiya da inshora na majalisar dattawa ta shirya a Abuja.

Ya ce hukumar ta raba wadannan kudade ne wa jihohi uku da suka cika sharuddan samun kudin tallafin kiwon lafiya wato BHCPF.

Wadannan jihohi kuwa sun hada da Abia,Osun da Ebonyi.

“ Akwai sharudda wanda ya kowacce jiha sai ta cika kafin ta samu kudin tallafin kiwon lafiya.

“Sai dai kuma akwai wasu sharudda da ya kamata su cika inda jihohi uku daga cikin 22 ne kawai suka kai ga haka.

Shugaban kwamitin inshora na majalisar Darlinton Nwokocha ya ce majalisar za ta fara gudanar da bincike kan matsalolin rashin samun kudade da fannin kiwon lafiya ke fama da su.

Nwokocha ya ce majalisar za ta yi haka ne bisa ga korafin da wasu masu ruwa da tsaki suke yi cewa fannin ba ta samun kudaden da gwamnati ta ware domin su.

“A yanzu haka majalisar ta ce wasu Naira biliyan 30 na nan ajiye a babbar bankin Najeriya da gwamnati ta ware a shekarar 2018 amma har yanzu fannin kiwon lafiya bata samu iya karbar ko sisi ba daga cikin kudaden.

Ya ce yin binciken zai taimaka wajen kawo karshen matsalolin rashin samun kudade a lokacin da ya kamata da fannin kiwon lafiya ke kuka da shi.

Share.

game da Author