Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, ta kama tsohon Gwamnan Jihar Abia, Orji Uzor Kalu da laifin zambar makudan kudade.
Mai Shari’a Mohammed Idris ne ya karanta hukuncin tuhumar da aka samu Kalu da laifi. Amma dai zuwa lokacin rubuta wannan labarin, ba a kai ga bayyana irin hukuncin da aka zartas a kan sa ba tukunna.
Jim kadan bayan da Mai Shari’a ya bayyana cewa an kama Kalu da laifin zambar kudaden, lauyoyin sa sun yi ta kokarin jan hankalin mai shari’a domin a zartas masa hukunci mai sauki.
Sama da shekara 10 kenan ake tafka shari’ar da aka gurfanar da Kalu kotu shi da kamfanin sa mai suna Slok Nig. Ltd.
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da shi, bisa zargin ya karkatar da bilyoyin kudade a lokacin da ya ke gwamna Jihar Abia tsakanin 1999 zuwa 2007.
Tun cikin watan Agusta ne dai Mai Shari’a Idris ya kammala sauraren karar, wadda sai a yau ne ya tabbatar da Kalu ya aikata laifin da EFCC ke zargin ya aikata.
A ranar 22 Ga Oktoba ne masu gabatar da kara da kuma lauyoyin Kalu suka kammala rufe bayanan su a rubuce, kuma Mai Shari’a y ace zai yanke hukunci a yau Alhamis, 5 Ga Oktoba.
PREMIUM TIMES Hausa za ta kawo muku yadda ta kwaranye a kotu, can an jima.
A zaman yanzu dai Kalu Sanata ne mai wakiltar Jihar Abia, a karkashin jam’iyyar APC kuma shine bulalar majalisar.