A cikin watan Agusta ne aka bankado harkallar kudaden Najeriya har dala $550,000 da ministan tsaron Kasa Bashir Magashi ya tafka a lokacin mulkin marigayi Sani Abacha.
Yau kwanaki 123 kenan cur da bankado wannan badakala amma fadar gwamnati ta yi tsit ba ta ce komai ba akai.
Bashir Magashi, shine ministan tsaron kasa Najeriya, kuma yana daga cikin ‘yan gaban goshin tsohon shugaban kasan Najeriya Marigayi Sani Abacha. Sai dai kuma kash, an gano yadda ya dulmiya hannayen sa cikin kwamacalar badakalar wawurar kudaden Najeriya da ya kai har dala 550,000 ya boye su a wani asusun ajiya a wani banki dake kasar Birtaniya.
Gwamnatin Obasanjo ne ta fara gano wannan badakalar kudade a lokacin da ta saka a gudanar da binciken kudaden da gwamnatin Abacha ta wawura a kasar nan.
A wannan bincike da shugaba Obasanjo ya saka mai ba shi shawara akan harkar tsaro, Abdullahi Sarki Mukhtar da wani dan kasar faransa da aka ba kwangilar yin bincike akai.
Sakamakon binciken da aka mika wa shugaban kasa a wancan lokaci Olusegun Obasanjo, ya nuna karara yadda Magashi ya kwashi nasa rabon cikin kudadan rarar mai da Abacha ya rika jida wa makusantarsa.
A binciken, an gano cewa wannan kudade an saka su ne a wani asusu a bankin kasar Birtaniya dauke da sunan Bashir Magashi.
Da gwamnatin Obasanjo suka nemi sanin ko me yasa Bashir ya boye wannan kudi sai ya roki cewa kada a kwace kudaden duka an rage masa na miya. Ya roki a bar masa dala 150,000, amma gwamnati ta kwace sauran.
Daga baya dai bisa ga bayanan da aka samu, haka akayi, gwamnati ta karbi dala 400,000, aka bar masa dala 150,000.
Sai dai kuma wakilin mu ya nemi ji daga bakin Obasanjo da tsohon mai bashi shawara, Sarki Mukhtar, amma dukkan su basu dauki waya ba sannan sakon da aka aika musu basu maido da amsa ba.
Shin Ko Buhari ya sanda haka kafin ya nada Magashi Minista?
Abinda ba a sani ba shine ko shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanda wannan cakwakiya kafin ya nada Magashi Ministan tsaron kasa?
An ne mi ji daga bakin kakakin shugaban kasa, Garba shehu amma hakan ya citura domin bai amsa kira ba sannan bai maido da amsar sako da aka aika masa ba.
Toh idan Buhari bai sani ba a matsayin sa na shugaban kasa ya kamata ace hukumar SSS sun iya ganowa cewa yana da guntun kashi a duwawu tunda sai sun yi binciken kwakwaf sannan su mika wa shugaban kasa kafin ya amince da nadin ministan.
Wani ma’aikacin fadar shugaban kasa da ya roki kada a bayyana sunansa ya ce a nasa ganin akwai yiwuwar cewa shugaba Buhari bai sani ba.
Ko da yake haka akayi badakalar tsohowar ministar kudi Kemi Adeosun da har yayi sanadiyyar ajiye aiki da ta yi.
Discussion about this post