Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), ta bai wa gwamnonin jihohi 36 wa’adin fara biyan mafi kankantar albashi zuwa nan da 31 Ga Disamba.
NLC ta yi wannan gargadin ne a taron da kungiyar ta yi domin tattauna yadda za ta kasance idan aka yi karin mafi kankantar albashi zuwa naira 30,000.
Daga cikin wadanda suka halarci taron, akwai shugabannin NLC na kasa, shugabannin NLC na kowace jiha, Kungiyoyin Kwadago daban-daban, Ministan Ingantuwar Aiki, Shugabannin Ma’aikata na kowace jiha da kuma wakilan Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO).
Bincike da nazari sun nuna cewa jihohi biyar ne kawai suka dan fara kamanta fara aiki da sabon tsarin albashi na mafi kankantar albashi zuwa naira 30,000.
Jihohin biyar kuwa sun kunshi Kaduna, Kebbi, Lagos, Adamawa da kuma Jigawa.
Sai dai kuma har yau ba a kai ga fara biyan a Jihar Jigawa ba, tun farkon lokacin da jihar ta cimma yarjejeniyar adadin da za ta rika biya a kowace wata.
A daya gefen kuma, akwai jihohi 13 da suka kafa kwanitin zaunawa da kungiyar kwadagon jiha domin a tattauna mafitar yadda za a saisaita tsarin biyan albashin, ta yadda za a fara biya.
Jihohin 13 sun hada da Borno, Abia, Kano, Bayelsa, Sokoto, Niger, Abia, Akwa Ibom, Edo, Ondo, Ebonyi, Katsina da kuma jihar Zamfara.
Har yau kuma NLC ta ce akwai wasu jihohi 19 da ba su fara shirin komai ba wajen batun fara biyan sabon tsarin albashi na naira 30,000 mafi kankanta.
Jihohin sun hada da Bauchi, Yobe, Rivers, Benue, Gombe, Kwara, Imo, Osun, Ekiti, Oyo, Anambra, Taraba, Cross River, Ogun, Enugu, Nasarawa, Plateau, Kogi da kuma jihar Delta.
Discussion about this post