Shugaban kungiyar likitoci ta Najeriya (NMA) Francis Faduyile ya bayyana cewa Najeriya za ta kwashe tsawon shekaru 25 tana daukar sabbin likitoci kafin ta iya daidai ta yawan mutanen ta da yawan likitocin da ke kasar.
Faduyile ya fadi haka ne a taron ma’aikatan kiwon lafiya da marubuta da aka yi a jihar Legas.
Taken taron shine ‘Samar da madafa kan yawan ficewar likitoci daga Najeriya zuwa kasashen waje’.
Ya ce matsalolin da suka hada da rashin biyan likitoci albashi mai tsoka,rashin kayan aiki da wuraren aiki,rashin wutar lantarki,rashin hanyoyi masu kyau,rashin ware wa fannin isassun kudade duk sune matsalolin da ake fama da su.
“Tsarin aiki da WHO ta tsara shine likita daya ya kula da marasa lafiya 600 sai dai hakan ba shine ke faruwa ba a Najeriya domin likita daya na kula da marasa lafiya sama da 10,000.
Ya kuma yi kira ga gidajen jaridu da su rika wayar da kan mutane game da kiwon lafiya a wajen rubuce rubucen su.
Bayan haka tsohon shugaban kungiyar likitocin dake aiki a asibitocin kudi na Najeriya Anthony Omolola ya bada kididdigar yawan adadin likitoci a Najeriya da ya ce sun kai akalla 72,000.
Omolola ya yi kira ga gwamnati da ta ware isassun kudade domin kula da fannin kiwon lafiya a kasarnan.
Ya ce yin haka zai taimaka wajen kawar da matsalolin karancin ma’aikata da ake fama da su a asibitocin.
A karshe shugaban kungiyar masana magungunan ta Najeriya (PSN) Sam Ohuabunawa ya yi kira ga kwararrun likitoci da su rika daurewa suna zama a kasar nan domin su taimaka wajen gina fannin kiwon lafiyar Najeriya.
Discussion about this post