Gwamnatin Jihar Kano ta haramta wa mace da namiji shiga Keke NAPEP, wanda a jihar aka fi sani da suna A Daidaita Sahu.
Sanarwar da wani jami’in gwamnatin ya fitar ta nuna cewa daga ranar 1 Ga Janairu ce wannan doka za ta fara aiki.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ne ya bayyana haka a lokacin da ake rufe wani taron sanin makamar aiki, IVC na Musulunci, wanda Kungiyar Dalibai Musulmi ta Shiyya, ta shirya a Jami’ar Bayero, Kano, ranar Laraba.
Kwamandan Hisba, Harun Ibn-Sina ne ya wakilci Ganduje a wurin taron, kuma shi ne ya yi sanarwar a wurin taron.
Ya ce Jihar Kano ta hana daukar mace da namiji a lokaci guda a cikin A Daidaita Sahu, ba a cikin birnin Kano kadai ba, har ma da dukkan sauran kananan hukumomi 44 na jihar baki daya.
Idan ba a manta ba, an shigo da keken A Daidata Sahu a matsayin keken sufurin haya mai daukar mata kadai, a lokacin mulkin tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau. Kuma tun a wancan lokacin ne aka sa masa sunan A Daidaita Sahu.
Gwamnatin Shekarau ta shigo da keken A Daidaita Sahu ne bayan ta haramta haya da babur.
A wurin taron dai Mai Martaba Sarkin Kano ya kara jan hankalin Musulmi su daina daukar hidimar abin da ya fi karfin su ko ka fi nauyin aljifan su.
Daga nan sai ya danganta yawaitar yara kanana da ke gararamba ba su zuwa makaranta, cewa yawan aure-auren mata da tara iyalin da namiji bai iya daukar nauyin su ne ke kara yawaitar irin wadannan yaran.