Gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya ya yaba bisa nasarorin da aka samu na dakile yaduwar cutar a jihar.
Yahaya ya fadi haka ne a wata takarda da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Ismaila Misilli ya saka wa hannu bayan taron ranar cutar da aka yi a Jihar.
Gwamnan yace sakamakon bincike ya nuna cewa jihar ta yi nasarar dakile yaduwar cutar daga 3.4 a shekaran 2017 zuwa 1.3 a 2019.
“Ina mika godiya ta ga hukumar hana yaduwar cutar kanjamau ta jihar Gombe (GomSaca) bisa kokarin da ta yi wajen ganin hakan ya tabbata a jihar.
“Daga nan kuma ina yi wa kungiyoyin kare hakin dan adam, shugabanin addinai, sarakunan gargajiya, ma’aikatan kiwon lafiya, gidajen jaridu, kungiyoyin bada tallafi na ciki da wajen kasar nan da masu ruwa da tsaki kan namijin kokarin da suka yi wajen ganin an samu nasarar haka.
Ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a jihar da su ci gaba da taimakawa jihar wajen ganin an cimma wannan buri.
Idan ba a manta ba a watan Maris ne Hukumar hana yaduwar cutar kanjamau ta kasa (NACA) ta gabatar da sakamakon binciken adadin yawan mutanen dake dauke da kanjamau a Najeriya.
Sakamakon bincike ya nuna cewa mutane miliyan 1.9 ne ke dauke da cutar kanjamau sannan masu shekaru 15 zuwa 49 ne suka fi yawa a dadain yawan masu dauke da cutar.
An gudanar da wannan bincike ne a shekaran 2018 sannan gwamnati ta yi haka ne domin inganta kula da masu dauke da kanjamau da Hepatitis B da C ke samu a kasan.
Sakamakon binciken ya kara nuna cewa mutane kashi 42.3 dake dauke da cutar ne ke samun kula inda daga ciki kashi 45.3 mata ne sannan kashi 34.5 maza.
Daga nan kuma an gano cewa yankin kudu maso kudu ce ta fi samu yawan mutanen dake dauke da cutar a kasar nan inda yawan su sun ya kai kashi 3.1.
A Yankin Arewa ta tsakiya mutanen dake dauke da cutar sun kai 0.2, kudu maso gabas kashi 1.9, kudu maso yama kashi 1.1, arewa maso gabas kashi 1.1 sannan arewa maso yamma kashi 0.6.
Discussion about this post