Mahara sanye da kayan sojoji sun yi garkuwa da Hakimin Birnin Gwari, Yahaya Abubakar, a hanyar a hanyar sa ta zuwa Birnin Gwari.
Haka kuma masu garkuwan sun arce da tsohon sakataren ilimi na karamar hukumar Ibrahim Musa, da ke tare da Hakimin a motar da aka yi garkuwa da su.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da aukuwar wannan mummunar Al’amari, inda ta sanr cewa an yi garkuwa da hakimin ne a kauyen unguwar Yako bayan wadannan mutane sun taida su.
Bayan haka Kakakin rundunar ya kara da cewa an yi garkuwa da wasu mutane uku a unguwan Sabon tasha dake Kaduna.
Wadanda aka yi garkuwar dasu sune, Jonathan Obi, Joakin Obi da Benjamin Obi. Ya ce dukkan su suna zama ne a unguwa daya.
” Bayan an sanar da rundunar yin garkuwa da wadannan mutane, jami’an mu sun fantsama cikin dazukan da ke zagaye da unguwar domin kamo wadanda suka aikata wadannan mahara.