Jam’iyyar APC ta koka kan tsare ‘ya’yan ta da gwamnatin Zamfara keyi

0

Shugaban jam’iyyar APC na jihar Zamfara Lawal Liman ya koka kan yadda ake yi wa ya’yan jam’iyyar dauki daidai ana garkame wa gidan kaso.

Liman ya bayyana haka ne da yake ganawa da shugabannin jam’iyyar na kananan hukumomin jihar a Gusau.

Ya ce bita da kulle ne kawai gwamnatin jihar karkashin mulkin PDP ke yi wa ‘yan APC din.

“Na jinjina wa ya’yan jam’iyyar mu a wannan jiha bisa jajircewa da suka yi sannan suka yi tsaye wajen ci gaba da mara wa jam’iyyar baya da yi mata aiki.

“Ina kuma kira a gare ku da kuga duk abin dake faruwa a matsayin gwaji ne daga wajen Allah.

Liman ya yi kira ga jami’an tsaro da su rika nisanta da shiga harkokin siyasa a jihar.

Idan ba a manta ba a makon da ta gabata ne Babbar Kotun Shari’a ta Zamfara ta sake garkame wani jigon dan siyasar Jihar Zamfara a kurkuku. An tura Bello Dankande gidan Yari bisa zargin sa da daukar nauyin ‘yan jagaliyar soshiyal midiya, su na yi wa gwamnatin jihar zagon-kasa.

‘Yan sandan da suka kama Dankande, sun je ne tare da sammacin umarnin kama shi daga kotu.

Sannan kuma ‘yan sanda sun zargi Dankande da laifin hada baki da ‘yan sa kai ana satar shanun Fulani a cikin Karamar Hukumar Bakura.

A kotu dai wanda ake zargin ya musanta dukkan cajin sa da ake yi a gaban alkali.

Sannan kuma lauyan sa mai suna Bello Gusau ya kalubalanci cewa wannan kotun ba ta da hurumin yi wa Dankande hukunci.

Sai dai kuma duk wannan bai hana mai shari’a ba da umarnin a kai Dankande gidan kurkuku a tsare, har zuwa ranar 12 Ga Disamba ba.

Share.

game da Author