Shugaban Hukumar shirya jarabawar shiga Jami’oi ta kasa JAMB, Ishaq Oloyode ya bayyana cewa daga yanzu hukumar baza ta rika ba ofisoshinta na jihohi naira miliyan 100 da take basu ada ba.
Oloyode ya fadi haka ne a zauren taro na Kongo dake jami’ar Ahmadu Bello a Zariya.
Ya ce sun gano cewa babu abinda ofisoshin ke yi da wadannan kudade da ke amfanar da hukumar ko ayyukanta.
” Tun daga shekarar 2016 muke aika wa jihohi naira miliyan 100. Ina so in sanar muku yau cewa mun dakatar da haka domin kusan duk abubuwan da suke yi da wadannan kudade kamfanonin masu zaman kansu da muke aiki tare ke yin su kuma suna samun riba masu yawa..
Oloyode ya kara da cewa sau da dama ana samun matsala a lokacin da dalibai ke yin rajistan jarabawar.
” Akwai matsala da muka samu a jarabawar bara inda mahaifiyar wata yarinya ta canja wa ‘yar ta darasin da take so ta karanta a jami’a. Sai bayan jarabawar ya fito ta je yin rajista a jami’ar da ta saka zabinta. Anan ne ta ga cewa ba abin da ta zaba bane aka bata. Da aka yi bincike akai sai aka gano cewa ashe mahaifiyar ta ce ta canja mata darasin bata sani ba.
Sannan kuma na tattauna da hukumar yi rajistar dan kasa, NIMC, game da yi wa daliban mu rajista da hukumar .
” Duk da cewa wasu na ta kokarin maido mana da hannun agogo baya wajen tilasta dalibai yin rajista da NIMC din a matsayin wani hanya da dole sai anyi kafin a iya zana rubutar JAMB da muka yi, muna ci gaba da nuna wa mutane cewa wannan shine hanya da da dole fa sai an bi.
Oloyode ya ce akalla kashi 40 bisa 100 na dalibai duk sun yi rajista da hukumar NIMC, sannan kuma sauran na kokarin ganin sun yi nasu rajistan.
Discussion about this post