INGANTA AYYUKAN NOMA: Gwamnati za ta kashe Naira biliyan 46.83 a yankin Neja-Delta

0

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za ta kashe akalla Naira biliyan 46.83 domin inganta aiyukan noma a jihohi tara na yankin Neja-Delta da wadanda ake hako danyen mai.

Wadannan jihohi sune Abia,Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River,Delta,Edo,Imo,Ondo da Rivers.

Ministan aiyukkan noma Sabo Nanono ya fadi haka a taron kaddamar da wannan shiri mai taken ‘Livelihood Improvement Family Enterprises (LIFE-ND) da aka yi a Fatakwal, jihar Ribas.

Ya ce gwamnati ta tsara wannan shiri ne domin samar da abinci da inganta tattalin arzikin kasa da na wannan yanki.

“Gwamnati za ta yi amfani da wadannan kudade wajen inganta kiwon kaji,kifi,noman kwakwan manja,rogo,shinkafa da ayaba. Sannan za ta yi kokarin kawar da matsalolin rashin kudin jari,rashin filin noma da rashin kasuwar amfanin gonan da aka noma a yankin.

Nanono ya ce shirin zai dauki tsawon shekaru 12 sannan hukumar raya yankin Neja-Delta (NDDC) da Asusun raya aiyukkan noma ta kasa da kasa (IFAD) za su hada hannu domin samar da kudaden da za a kashe a wannan shirin.

Ya yi kira ga mutanen yankin da su mara wa wannan shiri baya sannan kuma yayi alkawarin kirkiro irin haka a sauran yankunan kasarnan.

Bayan haka mataimakin shugaban NDDC Joi Nunieh ya ce shirin zai taimaka wajen inganta rayuwar mutanen Neja-Delta musamman wajen rage yawan hijira da mutane ke yi daga kauyuka zuwa birane.

A karshe Nunieh ya kara da cewa NDDC za ta bada gudunmuwar Naira biliyan 10.89 dimin nasarar shirin.

Share.

game da Author