Hukumar tsaro ta SSS ta saki mawallafin jaridar Sahara da ke tsare a hannun hukumar Yele Sowore.
An saki Sowore da misalin karfe shida na yammacin Talata a Abuja.
Hakan ya biyo bayan umarnin da Antoni Janar din Najeriya, Abubakar Malami ya baiwa hukumar SSS da ta saki Sowore da Sambo Dasuki.
Idan ba a manta ba a yammacin Talata ne hukumar SSS ta sanar da shirin sakin tsohon maiba shugaban kasa shawara kan harkokin Tsaro, Sambo Dasuki a lokacin mulkin Goodluck Jonathan da mawallafin jaridar Sahara Reporters da duk ke tsare.
Hukumar ta gayyaci lauyoyin Dasuki da Sowore su garzayo ofishinta maza-maza domin cika takardun sakin su.
Hukumar SSS ta tsare Dasuki tun a watan Disambar 2015 a bisa zargin harkallar dala biliyan 2 kudin makamai a lokacin mulkin Goodluck Jonathan.
Discussion about this post