A ranar Talata ne jamian hukumar EFCC suka damke sanata Shehu Sani a wani wuri a Abuja a bisa zargin hannu dumu-dumu a harkallar dala 10,000 da ya amsa da sunan zai mika wa shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu cin hanci.
Shi dai wannan kamayamaya da Shehu Sani ya fada ciki ya biyo bayan zargin karbar kudi ne har dala 10,000 da yayi a hannun fitaccen dan kasuwa ASD domin EFCC ta binciki wani tsohon sirikin sa da basu jituwa.
Wani jami’in EFCC da baya so a fadi sunan sa ya bayyana cewa tabbas an gano cewa sanata Shehu Sani ya karbi dala 10,000 domin ya ba Ibrahim Magu cin hanci.
Sai dai majiya a Kaduna ta sanar damu cewa sanata Shehu Sani ya maida wa ASD wannan kudi bayan ya tabbatar cewa harkallar ta tashi sannan ma EFCC ta gayyaci wannan dan kasuwa.
EFCC ta ce Shehu Sani ya yi kokarin kaucewa gayyatar hukumar inda ya kashe layin wayar da aka san sa da shi, amma kuma bayan haka an cafke shi a wani wuri a Abuja.
Jami’in hukumar ya shaida cewa za a gudanar da bincike domin gano ko tsohon sanatan yana amfani da sunan shugaban hukumar Ibrahim Magu wajen karbar kudade a hannun jama’a.
Duk da wannan zargi da muka jiyo, babu wanda ya amince a dauke shi a faifai, sannan kuma bamu iya tabbatar da wannan zargi ba kai tsayi fiye da cewa hukumar EFCC ta damke sanatan.
Mun yi ta kokarin kiran sa ta waya amma bai amsa kiran mu ba.
Discussion about this post