Hukumar Kididdigar Al’kaluman Tattalin Arziki ta Kasa (NBS), ta bayyana cewa Najeriya ta tara naira bilyan 275.12 a tsakanin Yuli zuwa Satumba, 2019.
Wannan adadin kudade dai ba su kai yawan wadanda aka tara tsakanin watannin Afrilu zuwa Yuni na 2019 ba.
A watannin Afrilu zuwa Yuni dai an tara naira bilyan 311.94 a matsayin kudaden VAT na wancan lokacin.
Hukumar NBS ta fitar da wannan sanarwa yau Litinin a Abuja, a lokacin da ta fitar da bayanan kudaden da ake tarawa a duk ratar tsawon watanni uku.
Ana daura watanni uku ana tarawa, sannan a bayyana abin da aka samu.
Haka kuma rahoton ya tantance cewa tsakanin Yuli zuwa Satumba na 2018, an tara naira bilyan 273.50.
Idan ba a manta ba, Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci masu tasarifin harkokin tattalin arzikin Najeriya su bijiro da hanyoyin kara samun kudaden shiga a kasar nan.
Ya ce za a rika biyan albashi da kudaden, maimakon a rika fita kasashen waje ana ciwo bashin da za a rika biyan albashi duk karshen wata.
A kan haka ne aka bijiro da karin harajin VAT, daga kashi 5 bisa 100 zuwa kashi 7.5 bisa 100.
Wannan na nufin nan da dan lokaci kadan harajin Vat zai karu saosai.
NBS ta ci gaba da bayyana dallla-dalla bangarorin da aka fi samun kudaden shiga, wato haraji daga wurin su.
Wasu da aka tara kudade a bangaren su, sun hada da ayyukan yau da kullum, kayan dinka suturu, masana’antun yin tufafi, magunguna, sabulai da sauran nau’ukan kayan ban-daki da sauran su.